Gwamnatin jihar Borno ta kara kwanaki 7 kan dokar hana fita da ta sa a Maiduguri

Gwamnatin jihar Borno ta kara kwanaki 7 kan dokar hana fita da ta sa a Maiduguri

Gwamnatin Borno ta sanar da tsawaita dokar hana fita daga karfe 8 na maraice zuwa karfe 6 na safe a Maiduguri har na tsawon kwanaki bakwai.

A wani jawabi da kwamishinan yada labarai ya gabatar, a ranar Juma’a a Maiduguri yace an daga dokar hana fitan zuwa 20 ga watan Janairu.

Bulama ya bayyana cewa matakin zai samar ma rundunar sojoji isasshen lokaci don karkare aiki na musamman da suke yi akan Boko Haram da kuma cin gajiyar nasara da akayi akansu zuwa yanzu.

Gwamnatin jihar Borno ta kara kwanaki 7 kan dokar hana fita da ta sa a Maiduguri

Gwamnatin jihar Borno ta kara kwanaki 7 kan dokar hana fita da ta sa a Maiduguri

Ya bayyana cewa gwamnatin na takaicin rashin walwala da takura da hakan ke haifarwa ga mutane.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Kotun daukaka kara ta dakatar da dan majlisa, ta yi umurnin sake sabon zabe

Bulama ya kara da cewa an dauki matakin ne domin tabbatar da tsaro a gaba daya jihar da kuma jin dadin mutane.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel