Matasan APC suna son gwamnati ta haramta makarantun kudi

Matasan APC suna son gwamnati ta haramta makarantun kudi

- Matasan jam'iyyar APC reshen jihar Kaduna tayi kira ga gwamnati ta haramta dukkan makarantun kudi a jihar

- Matasan sun bayyana hakan ne a lokacin wata tataki da suka yi domin nuna goyon bayan su ga gyare-gyaren da Gwamna El-Rufai keyi a fannin ilimi a jihar

- Sun bayyana cewa makarantun kudin ne ke asasa banbanci tsakanin ilmin da 'ya'yan masu kudi da na talakawa ke iya samu

Kungiyar matasan jami'iyyar APC yankin Arewa maso Yamma sun bukaci gwamnatin Tarayya ta haramta makarantun kudi a duk fadin kasar nan.

Sun bayyana hakan ne a ranar Juma'a 12 ga watan Janairu a inda suka shirya wata tataki domin nuna goyon bayan su ga gyare-gyren da gwamna El Rufai ya ke a fannin Ilimi.

Sun bayyana cewa gyare-gyaren ya zama dole har idan an bukatan ceto makarantun gwamnati daga rugujewa baki daya kamar yadda kamfanin dillanci labarai na kasa NAN ta ruwaito.

Matasan APC suna son gwamnati ta haramta makarantun kudi

Matasan APC suna son gwamnati ta haramta makarantun kudi

Sakataren kungiyar matasan, Mallam Isiyaku Sarkin Pawa yace ya zama dole Najeriya ta dauki matakai domin ceto fanin ilimi a kasar nan har idan ana son a gina kasar ingantaciya.

DUBA WANNAN: Dubi wata karamar yarinya mai shudin idanu da ake zargi da maita

Ya kara da cewa makarantun gwamnati yanzu sun zama na talakawa ne kawai sabanin da kuma hakan na kara asasa tsaikon damar samun ingantacen ilimi tsakanin yayan masu kudi da na talakawa.

Kwamishinan kananan hukumomin da sarautu, Ja'afaru Sani wanda ya tarbi tawagar matasan a madadin gwamna El-Rufai yace garambawul din da gwamna ke yi a jihar don siyasa bane, yana yi domin dawo da martabar da amfanar zuri'ar da za su biyo bayan mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel