Nigerian news All categories All tags
Dakarun Najeriya da Kamaru sun hada gwiwar yaki da ta'addanci

Dakarun Najeriya da Kamaru sun hada gwiwar yaki da ta'addanci

Ministan tsaro na Najeriya, Mansur Dan-Ali ya bayyana cewa dakarun Najeriya da na Kamaru sun hada gwiwa wajen gudanar da yaki da ta'addanci a yankunan Arewa maso Gabashin kasar nan.

Ministan ya bayyana hakan ne a babban masallacin kasar nan dake birnin tarayya, bayan an kammala sallar ta Juma'a ta yau.

A wata ganawa da manema labarai na jaridar Daily Trust, Dan-Ali ya bayyana cewa babu shakka akwai nasarori da aka samu a sakamakon hadin gwiwar dakarun kasar nan da kuma na kasar Kamaru wajen ci gaba da yakar ta'addanci a yankunan Kudu maso Gabashi.

Dakarun Soji

Dakarun Soji

A yayin tuntubarsa dangane da rikice-rikice dake kunno kai a cikin kasar nan, Mansur ya tabbatar da cewa dakarun Najeriya a shirye suke wajen baiwa kasar nan kariya duba da kalubalen tsaro da take fuskanta a cikin wasu sassanta.

KARANTA KUMA: Shugaban shi'a El-Zakzaky bai mutu ba, yana nan a raye - IMN

A tasa ganawar da 'yan jarida, ministan harkokin cikin gida, Abdulrahman Dambazau ya bayyana cewa, a duk ranar 15 ga watan Janairun kowace shekara, za a rinka tunawa da kuma jinjinawa jarumta da sadaukar da kai na dakarun tsaro a fadin kasar nan.

Dambazau ya kara da cewa, gwamnati tana iyaka bakin kokarinta wajen fadi tashin samar da madafan dogaro na magance matsalolin tsaro a kasar nan.

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel