Yadda mu ka kama Desmond Okutubo, babban dan kungiyar Don Wanny – Yan sanda

Yadda mu ka kama Desmond Okutubo, babban dan kungiyar Don Wanny – Yan sanda

Rundunar yaan sandan Najeriya ta yi Karin haske kan yadda ta kama Desmond Okutubo, dan kungiyar asiri kuma babban mamba na kungiyar masu garkuwa da mutane da suka kaddamar da kisan mutane 20 a ranar sabon shekara a garin Omoku, jihar Rivers. Don Wanny, wanda tuni aka aika shi lahira ne ya jagoranci harin.

Wata sanarwa daga Jimoh Moshood, kakakin rundunar yan sanda, ya yi bayanin cewa an kama Okutubo ne da taimakon sashin bincike nay an sanda, wanda suka hada da tawagar kwararu na babban sufeto nay an sanda, da kuma sashin ayyuka da hukumar yan sandan jihar Rivers.

A cewar sanarwan, sufeto janar nay an sanda ne ya bayar da umurni kan ayi gaggawan gano wadanda suka yi kisan.

Sakamakon wannan umurni, tawagar kwararru na IGP tare da hadin gwiwar sashin bincike na musamman suka farma wasu da ake zargi a mafakarsu dake dajin Awara tsakanin jihohin Imo da Rivers.

Yadda mu ka kama Desmond Okutubo, babban dan kungiyar Don Wanny – Yan sanda

Yadda mu ka kama Desmond Okutubo, babban dan kungiyar Don Wanny – Yan sanda

A musayar wuta da ya dauki tsawon wasu awanni, anyi nasarar kashe mutane shida daga tawagar yayin da sauran suka tsere zuwa garuruwan Rivers, Delta, Imo da Bayelsa da raunuka, inda yan sanda ke farautarsu a yanzu.

Yan sandan sun kara da cewa tawagar kwararu na IGP dun gano Okotubo wanda ya tsere Abuja a ranar 3 ga watan Janairu bayan musayar wuta ta hanyar amfani da kwararren dabaru. An kama shine a Mpape dake Abuja a ranar 9 ga watan Janairu.

KU KARANTA KUMA: Har yanzu ba a ga bayan Boko Haram ba - Majalisar Dinkin Duniya

Okotubo mai shekaru 32 ya fito ne daga karamar hukumar Unelga dake jihar Rivers. Ya kuma tona asirin cewa yana daya daga cikin wadanda suka kaddamar da kisan Omoku.

Okutobo ya ce kusan su 30 ne suka kaddamar da kisan. Sun yi amfani da bindigogin AK-47 guda 20, sun ketare ruwa daga Awara zuwa dajin Omoku sannan suka shiga garin Omoku, inda suka kashe mutanen dake dawowa daga coci. Ana ci gaba da gudanar da bincike domin kama sauran tawagar. Za a gurfanar da Okutubo a kotu bayan kammala bincike.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel