Nigerian news All categories All tags
Jam’iyyar ADP ta ki amince da tsarin zaben 2019 da INEC ta fitar

Jam’iyyar ADP ta ki amince da tsarin zaben 2019 da INEC ta fitar

- Jam’iyyar ADP ta nuna rashin amincewar ta ga tsarin zaben 2019 da INEC ta fitar

- Shugaban jam’iyyar ya soki lamirin yadda hukumar ta shirya zaben shugaban kasa kafin na gwamnatoci

- Shugaban ya ce APC ta shirya makirshi don tafka magudi a zaben shekarar 2019

Jam’iyyar ADP ta ki amince da lokuta da tsarin aiki wanda hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta bayar a ranar Talata 9 ga watan Janairu.

Majiyar Legit.ng ta tabbatar cewa, shugaban jam’iyyar na kasa, Injiniya Yabaji Yusuf Sani, ya sanar da wannan ci gaba yayin da yake hira da manema labarai a ranar Alhamis, 11 ga watan Janairu a Abuja, babban birnin kasar.

Legit.ng ta tattaro cewa Sani ya soki lamirin yadda hukumar ta shirya zaben shugaban kasa kafin na gwamnatoci.

2019: Jam’iyyar ADP ta ki amince da tsarin zaben da INEC ta fitar

Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu

Hukumar zabe ta saka ranar zaben shugaban kasa da na majalisar tarayya ranar Asabar, 16 ga watan Fabrairu, 2019, yayin da ta shirya na gwamnatoci ranar Asabar, 2 ga watan Maris, 2019.

KU KARANTA: Rikicin APC a Kano: Wata kungiya ta bukaci hukuma ta bincike Abbas

Sani ya bukaci halin da za a fara gudanar da zaben majalisun jiha sa’a nan a kammala da zaben shugaban kasa.

Shugaban ADP ya yi zargin cewa jam'iyya mai mulki ta APC ta shirya makirshi don tafka magudi a zaben shekarar 2019.

Ya ce: "Yadda hukumar INEC ta tsara zaben 2019 ba ta muna dadi ba saboda idan aka samu wanda ya lashe kujerar shugaban kasa, to, zai iya abin da ya gadama”.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel