Mun tsaya daram dam-dam akan takaran shugaba Buhari a 2019 - Gwamnoni Arewa

Mun tsaya daram dam-dam akan takaran shugaba Buhari a 2019 - Gwamnoni Arewa

- Shugaba Muhammadu Buhari ya fito Sallar Juma'a inda ya tarbi gwamnonin jihohin Arewa 7

- Bayan Sallar Juma'a, shugaba Buhari yayi ganawar sirri da su

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya halarci Sallar Juma'a a yau Juma'a, 1 ga watan Junairu, 2018 a Masallacin fadar shugaban kasa da ke babban birnin tarayya Abuja. Daga cikin wadanda suka halarci fadar a yau sune gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai; gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello; gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje; da gwamnan jihar Bauchi, Mohammad Abubakar.

Yayinda sukayi jawabi ga manema labarai bayan ganawar da sukayi kimanin sa'o'i 2, gwamna El-Rufa'i ya ce suna son shugaba Buhari ya sake takara a 2019.

Mun tsaya daram dam-dam akan takaran shugaba Buhari a 2019 - Gwamnoni Arewa

Mun tsaya daram dam-dam akan takaran shugaba Buhari a 2019 - Gwamnoni Arewa

Yayinda aka tambayeshi a kan cewa sun kawo ziyaran don zaben 2019 ne, El -Rufa'i yace: "Mun yan siyasa ne, kuma duk wanda ka gani a nan na son shugaban kasa ya sake takara a 2019. Babu ja da baya."

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya halarci Sallar Juma'a tare da gwamnoni

"Munada imani a kan shugaban kasa, muna son ya cigaba da gudanar da al'amuran kasan nan yadda ya kamata. Mutane na da yancin hasashe akan 2019."

Kowa nada ra'ayinsa amma a matsayinmu na gwamnoni, dukkanmu karon mu na farko kenan a shugabanci sabanin gwamnan jihar Yobe. Muna goyon bayan cigaban shugaba Buhari."

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a

http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel