Har yanzu ba a ga bayan Boko Haram ba - Majalisar Dinkin Duniya

Har yanzu ba a ga bayan Boko Haram ba - Majalisar Dinkin Duniya

- Mataimakiyar sakataren majalisar dinkin duniya, Amina ta yi tsokaci akan yaki da ta’addanci a kasar

- Amina Mohammed ta ce duk da tarin nasarori da sojojin Najeriya ke samu akan yan taáddan har yau yan ta’addan basu kare ba

- Tsohuwar ministar muhallin ta jadadda cewa Majalisar Dinkin Duniya za ta tallafawa Najeriya sosai

- Ta kuma yaba ma gwamnatin tarayya da na jihar Yobe kan kokarinsu

Mataimakiyar sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Amina J Mohammed, ta sanar da cewa duk da tarin nasarar da sojojin Najeriya su ka yi wajen hana hare-haren ta’addanci a yankin arewa maso gabashin kasar, to maganar gaskiya ita ce har yau ba a ga bayan Boko Haram ba.

Amina wacce ta kasance tsohuwar ministar muhalli a gwamnatin Shugaba Buhari, ta ce Majalisar za ta tallafawa Najeriya sosai a wannan shekara saboda tabbatar da an kara samun gagarimin nasara.

Ta yi wannan jawabi ne a lokacin da ta kai ziyara ofishin Gwamnan Jihar Barno, Kashim Shettima, daidai lokacin da ta kammala ziyarar kwanaki biyu da ta kai jihar.

Har yanzu ba a ga bayan Boko Haram ba -Majalisar Dinkin Duniya

Har yanzu ba a ga bayan Boko Haram ba -Majalisar Dinkin Duniya

Ta yaba wa gwamnatin tarayya da ta jihar Yobe musamman ganin irin kokarin da ta yi wajen sake gina al’ummomin da Boko Haram ta cika da su.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari ya yi ganawar sirri da gwamnonin arewa 7

Amina ta ci gaba da cewa akwai bukatar kara yin hobbasa wajen inganta hanyoyin da ake taimaka wa sojoji su na gudanar da farmaki kan Boko Haram, musamman a tabbatar su na da kayan fama da suka dace da kuma alaka tsakanin su da fararen hula da sauran hukumomin tsaron kasar nan.

A cewarta hakan zai taimaka wa sojoji matuka wajen sanin irin yanayin da wasu jama’a da ke inda aka giggirke jami’an tsaron ke ciki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel