Yanzu Yanzu: Kotun daukaka kara ta amince da umurnin kwace N4.5b na Patience Jonathan

Yanzu Yanzu: Kotun daukaka kara ta amince da umurnin kwace N4.5b na Patience Jonathan

- Kotun daukaka kara ta amince da umurnin kwace kudaden Patience Jonathan

- Kotun ta yarda da mallakawa gwamnatin tarayya kimanin dala biliyan 5.8 (Naira biliyan 2.1) da kuma wani kudi naira biliyan 2.4 da aka gano a asusun bankin uwar gidan tsohon shugaban kasa

- Kotun ta kori karar da aka daukaka akan Patience a ranar Juma’a, 12 ga watan Janairu

Kotun daukaka kara ta yarda da wani umurni na kwace dala miliyan 5.8 (naira biliyan 2.1) da kuma wani naira biliyan 2.4 da aka gano a asusun uwargidan tsohon shugaban kasa, Patience Jonathan.

Kotu ta kori karar da tawagar kare Patience karkashin jagorancin wani babban lauyan Najeriya, Mike Ozekhome suka gabatar a gabanta.

Idan zaku tuna hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta zargi uwargidan tsohon shugaban kasar da satar wasu makudan kudi da ya kai kimanin dala miliyan 15.5 daga gwamnatin tarayya da hukumominta.

Yanzu Yanzu: Kotun daukaka karat a tsayar da umurnin kwace N4.5b na Patience Jonathan

Yanzu Yanzu: Kotun daukaka karat a tsayar da umurnin kwace N4.5b na Patience Jonathan

Kungiyar yaki da rashawar ta roki kotu da ta daskarar da asusun uwargidan tsohon shugaban kasar yayin da ta bayyanawa kotun cewa Patience bata gudanar da ko wani kasuwanci ba wanda zai bata damar mallakar irin wannan makudan kudade.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari ya yi ganawar sirri da gwamnonin arewa 7

Hukumar ta EFCC ta kuma bayyana cewa kudin ba mallakar uwargidan tsohon shugaban kasar bane kamar yadda bincike ya nuna cewa an saci kudin ne daga gwamnatin tarayya da hukumominta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel