Yanzu Yanzu: Buhari ya yi ganawar sirri da gwamnonin arewa 7

Yanzu Yanzu: Buhari ya yi ganawar sirri da gwamnonin arewa 7

A ranar Juma’a, 12 ga watan Janairu, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da gwamnonin bakwai daga yankin arewacin kasar a cikin sirri a fadar shugaban kasa yan sa'o'i kadan bayan sallar Juma’a.

Gwamnonin da suka halarci ganawar sun hada da na jihohin Kaduna, Yobe, Kogi, Niger, Plateau, Adamawa da kuma Kano.

Da yake jawabi ga manema labaran fadar shugaban kasa, gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai, ya ce ba laifi bane don sun gana da shugaban kasar kan zaben shugabancin kasa na 2019.

Yanzu Yanzu: Buhari ya yi ganawar sirri da gwamnonin arewa 7

Yanzu Yanzu: Buhari ya yi ganawar sirri da gwamnonin arewa 7

Ba’a bayyana cikakken rahoton ganawar ba a daidai lokacin kawo wannan rahoto.

KU KARANTA KUMA: Ka saki Sambo Dasuki da El-Zakzaky yanzu – HURIWA ga Buhari

Yanzu Yanzu: Buhari ya yi ganawar sirri da gwamnonin arewa 7

Shugaba Buhari bayan sallar Juma'a

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel