Nigerian news All categories All tags
Karya ne, ba'a kwantar da uwargidan shugaba Buhari ba - Shugaban Asibitin Cedarcrest

Karya ne, ba'a kwantar da uwargidan shugaba Buhari ba - Shugaban Asibitin Cedarcrest

- Dan shugaba Buhari, Yusuf Buhari, dai ya samu hadari ne sanadiyar wasa da babur tare da wani abokinsa a cikin garin Abuja

- An sallami Yusuf Buhari a yau Juma'a, 12 ga watan Janairu daga asibitin Cedarcrest

- Rahotanni sun yadu a kafafen yada labarai cewa Aisha Buhari ya yanke jiki ta fadi sanadiyar hadarin yaron ta

Shugaban Asibitin Cedarcrest Hospital, Abuja, Dr. Felix Ogedegbe, ya musanta rahotannin da ke rada cewa an kwantar da uwargidan shugaba Buhari, Aisha Buhari, a asibitin sanadiyar yanke jiki bayan samun labarin hadarin danta, Yusuf Buhari.

Shugaban asibitin ya bayyana cewa an kwantar da Yusuf Buhari ne a asibitin su na Cedarcrest Hospital, Abuja sanadiyar raunukan da ya samu a wani mumunan hadarin babur kuma za'a sallame shi.

Karya ne, ba'a kwantar da uwargidan shugaba Buhari ba - Shugaban Asibitin Cedarcrest

Karya ne, ba'a kwantar da uwargidan shugaba Buhari ba - Shugaban Asibitin Cedarcrest

Kana Dr. Ogedegbe ya musanta rahotannin cewa wani abokin Yusuf Buhari ma ya kwanta a asibitin. A wata jawabin da aka samu daga bakin mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina, ya ce ai ba zai yiwu ma asibitin ta dinga bada amsa kan wasu maganganu da ke yaduwa ba amma kawai sunyi magana akan na cewa an kwantar da uwargidan shugaban kasa.

Yace: " Mun samu rahotanni iri-iri a kan hadarin amma ba zai yiwu ma mu dinga mayar da martani kan su ba".

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya halarci Sallar Juma'a tare da gwamnoni

Yanzu dai ana sa ran Yusuf Buhari ya samu sauki kuma an kai shi gida bayan sallama daga asibiti.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a

http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel