Nigerian news All categories All tags
Kotu ta gurfanar da wani mutum da ya gutsure karan hancin matarsa a jihar Legas

Kotu ta gurfanar da wani mutum da ya gutsure karan hancin matarsa a jihar Legas

Wata kotun majistire dake jihar Legas, ta bayar da umarnin tsare wani mutum dan shekaru 34 a gidan kaso na Ikoyi bisa aikata laifin cin zarafin matarsa, Bukola tare da gutsure mata karan hanci da hakori.

Bisi Adebiosu, wanda mazaunin Lagos Island ne yana fuskantar laifuka biyu ne da kotun da rataya a wuyansa.

Sufeto Nurudeen Thomas, jami'in dan sanda mai shigar da kara a gaban kotu ya bayyana cewa Bisi ya aikata laifin ne a ranar 9 ga watan Janairu a gidansu na aure.

Yake cewa, bayan da Bisi ya lakadawa uwar 'ya'yansu dukan tsiya ya kuma sanya hakwara wajen gutsure karan hancin ta wanda wannan laifin ya sabawa sashe na 176 na kundin dokokin jihar, kuma hukunci dauri ne har na tsawon shekaru biyar ko kuma zabi na biyan diyyar Naira dubu ɗari.

Kotun Shari'a

Kotun Shari'a

Mista Bisi ya labartawa kotun yadda hakan ta kasance bayan dawowarsa gida daga kasuwa, sai ya riski 'ya'yansu biyu suna rusa kuka kuma da ya tambayi inda mahaifiyarsa take sai suka ce ai ta shiga makota casu.

KARANTA KUMA: An sace jariri a wani asibitin jihar Kaduna

Ya ci gaba da cewa, isarsa wannan gida ke da wuta ya riski matarsa a tsakankanin maza tana ta dibar barasa, inda a yayin tursasa ta na cewar sai ta koma gida ne ya fusata wajen gutsure mata karan hanci.

Ita kuwa alkaliyar kotun, Misis Kikeloma Ayeye, ta bayar da umarnin a ci gaba da tsare wannan mutum a gidan kaso har zuwa ranar 12 ga watan Fabrairu domin ci gaba da sauraron karar.

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel