Nigerian news All categories All tags
Rikicin APC a Kano: Wata kungiya ta bukaci hukuma ta bincike Abbas

Rikicin APC a Kano: Wata kungiya ta bukaci hukuma ta bincike Abbas

- Wata kungiya mai zaman kanta tayi kira ga hukumomin tsaro su bincike Alh. Abdullahi Abbas Sanusi bisa kalaman da ya fada a faifan bidiyo

- Kungiyar tace abin takaici ne babban Jami'in gwamnati kaman sa ya fito yana asasa matasa su tada fitina ta hanyar jifar Sanata Rabiu Kwankwaso idan ya kawo ziyara jihar

- Kungiyar tace idan ba'a gudanar da sahihiyar bincike kuma an hukunta masu hannu cikin fitinar ba, hakan na iya gurguntar da demokradiya a jihar

Wata kungiya mai zaman kanta 'Centre for Information technology and Development' (CITAD) a Kano tayi kira ga hukumomin tsaro da su bincike kwamishinan ayyukan na musamman na jihar, Alhaji Abdullahi Abbas Sanusi domin yayi karin haske kan kira da yayi ga matasan Kano su jefi tsohon gwamna Sanata Rabiu Musa Kwankwaso idan ya kawo ziyara jihar.

Rikicin APC a Kano: Wata kungiya ta bukaci hukuma ta bincike Abbas

Rikicin APC a Kano: Wata kungiya ta bukaci hukuma ta bincike Abbas

DUBA WANNAN: Dubi wata karamar yarinya mai shudin idanu da ake zargi da maita

A jawabin da yayi a taron manema labari da ya kira, babban jami'in shirin wanzar da zaman lafiya na kungiyar, Malam Isah Garba ya bayyana rikicin da ke tsakanin magoya bayan Gwamna Abdullahi Ganduje da kuma Sanata Rabiu Kwankwaso a matsayin abu mai hatsari da ka iya gurgunta demokradiya a kasar nan.

Ya ce abin takaici ne da kuma hatsari yadda babban jami'in gwamnati kamar kwamishinan ya bude baki ya ce matasa su jefi Sanata Kwankwaso bayan ya kira shi shedanin siyasa. Ya kuma ce kwamishinan ya bayyana a kaikace cewa yana da hannu cikin rura wutar rigimar da kaure a Minjibir da kuma rikicin da akayi a ranar Hawan Daushe wanda yayi sanidiyar raunana mutane da yawa.

Kungiyar ta ce idan ba'a bincike al'amarin ba kuma na hukunta wadanda ke da hannu ciki, hakan na iya kawo cikas ga zaman lafiya da aka dade ana mora a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel