Daga karshe! An saki yar tsohon gwamna bayan ta shafe kwanaki 90 a gidan yari, ta aika sako ga gwamnati (bidiyo)

Daga karshe! An saki yar tsohon gwamna bayan ta shafe kwanaki 90 a gidan yari, ta aika sako ga gwamnati (bidiyo)

Rahotanni sun kawo cewa daga karshe rigimammiyar yar jaridar nan ta Najeriya Kemi Omololu-Olunloyo ta samu yanci bayan ta shafe tsawon kwanaki 90 a gidan yarin Port Harcourt.

Yan awanni bayan sakin nata, yar tsohon gwamnan a ranar Talata, 9 ga watan Janairu ta je shafinta na Instagram inda ta wallafa wani bidiyon godiya ga masoyanta da masu mara mata baya kan kasancewa da sukayi tare da ita a lokacin da take cikin mawuyacin hali.

Daga karshe! An saki yar tsohon gwamna bayan ta shafe kwanaki 90 a gidan yari, ta aika sako ga gwamnati (bidiyo)
Daga karshe! An saki yar tsohon gwamna bayan ta shafe kwanaki 90 a gidan yari, ta aika sako ga gwamnati

Ta ci gaba da cewa an sake ta da misalin karfe 5:30 na yammacin wannan rana da ta wallafa bidiyon. Olunloyo ta ci gaba da bayanin cewa akwai bukatar gwamnatin tarayya tayi gaggawan kula da fursunoni domin lafiyarsu na tabarbarewa a kullun.

KU KARANTA KUMA: Aminu Sanusi ya kama aiki gadangadan a matsayin dan sanda (hotuna)

A ranar Laraba, 10 ga watan Janairu, Kemi Olunloyo ta je shafinta na Instagram domin gode ma shahararren dan wasan babur dinnan Charly Boy bisa goyon bayanshi gare ta a lokacin da take kulle.

Ga abun da ta wallafa a kasa:

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel