Nigerian news All categories All tags
Buhari ya raba ma Obasanjo, Abdulsalam, Gowon, Jonathan maƙudan miliyoyin Nairori

Buhari ya raba ma Obasanjo, Abdulsalam, Gowon, Jonathan maƙudan miliyoyin Nairori

Gwamnatin tarayya ta kammala shirin biyan tsofaffin shuwagabannin kasar Najeriya makudan kudi da suka kai naira miliyan 280 don siyar motocin alafarma, idan har suna bukata, inji rahoton Punch.

Gwamnati ta tanadi wannan kudi ne a cikin kasafin kudin bana, inda zuwa yanzu an sakar ma tsofaffin shuwagabannin kimanin naira miliyan 40, nan bada dadewa ba kuma za’a cika musu sauran miliyan 240.

KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun rugurguza gidan fitaccen mai garkuwa da mutane, Don Wayne

Daga cikin tsofaffin shuwagabannin da zasu amfana da wannan garabasa sun hada da Alhaji Shehu Shagari, Cif Olusegun Obasanjo, Janar Yakubu Gowon, Abdulsalam Abubakar, Ibrahim Badamasi Babangida da kuma Ernest Shonekan.

Buhari ya raba ma Obasanjo, Abdulsalam, Gowon, Jonathan maƙudan miliyoyin Nairori

Tsofaffin shuwagabannin kasa

Haka zalika suma tsofaffin mataimakan shuwagabannin kasa da suka hada da Atiku Abubakar, Alex Ekwueme, Namadi Sambo da saura wadanda suka yi a zamannin mulin Soja duk zasu amfana da wannan yayyafin alheri.

Majiyar Legit.ng ta samu dukkanin bayanan nan ne daga bakin sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha a yayin da yake mayar da jawabi ga kwamitin majalisar wakilai mai kula da al’amuran gwamnati kan kasafin kudin fadar shugaban kasa a ranar Talata 9 ga watan Janairu.

Mustapha ya bayyana cewa gwamnati zata kashe naira miliyan 96 wajen siyan motocin tsofaffin shuwagabannin kasa, yayin da za’a kashe naira miliyan 90 ga mataimakansu, sai dai an yanke shawarar basu kudaden don siyan motar da suka fi so.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel