David Mark, na uku a Najeriya a zamanin PDP, na ganin tasku a mulkin jam'iyyar APC

David Mark, na uku a Najeriya a zamanin PDP, na ganin tasku a mulkin jam'iyyar APC

Tun saukarsu daga mulki a zamanin PDP, kuma bayan shafe shekaru 8 yana shugabantar majalisar dattijai, ya fara ji a jika, a mulkinn adawa, soja da ya shiga siyasa bayan ajje khaki, yanzu dai yana dandana kudarsa

David Mark, na uku a Najeriya a zamanin PDP, na ganin tasku a mulkin jam'iyyar APC

David Mark, na uku a Najeriya a zamanin PDP, na ganin tasku a mulkin jam'iyyar APC

David Mark, mai shugabantar majalisar dattijai 2007-2015, a baya ana yi masa ma ganin shi zai gaji Jonathan, saboda ganin shakuwarsu, da ma kuma irin karin fada aji da yake da shi a zamanin.

Ya dai fito daga jihar Binuwai, jiha da bata taba bada shugaban kasa ba, kuma yanki ne na tsakiyar Najeriya, wanda kiristoci suke da karfin fada aji.

DUBA WANNAN: Tahirin Dakta Mamman Shata

Sai gashi rahotanni na nuna cewa, an baiwa dattijon wa'adin makonni ukku ya tattara ya fice daga gidan shugaban majalisar wanda ke Apo Legislators Quarters, wanda ya sayar wa da kansa kan naira miliyan 650, kasa da kudin gidan a kasuwa.

David Mark, na uku a Najeriya a zamanin PDP, na ganin tasku a mulkin jam'iyyar APC

David Mark, na uku a Najeriya a zamanin PDP, na ganin tasku a mulkin jam'iyyar APC

Gwamnatin APC dai ta tuhume shi da cin hanci da rashawa, an kuma kwace masa fasfo tun 2015, haka ma dai, gwamnatin tana kan bincikarsa kan kudaden zabe da na makamai, da wadanda ya kashe a lokacin yana shugabantar majalisa.

A karshe ma dai, tunda jihar tasa tana hannun jam'iyya ta adawa, hasashe na nuna da kyar in gwamnan jihar zai bashi ya kai da kujerar tasa ta zaman majalisa mai jar kujera.

Lallai zamani in ya juya maka baya sai hakuri.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel