Nigerian news All categories All tags
Wani manazarci ya yi ikirarin Gwamnonin APC 8 da Sanatoci za su bi Atiku zuwa PDP

Wani manazarci ya yi ikirarin Gwamnonin APC 8 da Sanatoci za su bi Atiku zuwa PDP

- Manazarci ya sakankance Gwamnoni 8 da Sanatoci 22 da 'Yan Majalisu 66 za su bi Atiku zuwa PDP

- Ya ce za su yi wannan canjin shekar ne nan da karshen watan Fabrairu na 2018

- Ya kuma ce Atiku mutum ne mai gaskiya wanda ba zai ji shayin fadawa Buhari kuskuren sa ba

Wani manazarci mai suna Sunny Onuesoke, wanda kuma ya nemi tsayawa takaran gwamna a 2007, karkashin inuwar PDP, ya bayyana ra'ayin sa game da canjin shekar Atiku daga APC zuwa PDP.

Onuesoke ya kuma nuna farin cikin sa game canjin shekar Atikun. Ya ce komowar na sa zuwa PDP zai kara ma ta karfi. A cewar sa, hakan zai sa manyan 'yan siyasa irin su Tinubu za su biyo shi zuwa PDP.

Gwamanoni 8 da wasu sanatoci da za su bi Atiku, inji wani mai nazirin siyasa

Gwamanoni 8 da wasu sanatoci da za su bi Atiku, inji wani mai nazirin siyasa

Ya kuma sakankance nan da zuwa karshen watan Fabrairu na Gwamnoni 8 da Sanatoci 22 da 'Yan Majalisu 66 na APC za su koma jam'iyyar PDP. Ya kuma yi ikirarim cewa tuni 2 daga cikin Gwamnonin su ka bayyana kudirin su na komawa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

A game da batun ko Atiku zai samu lashe zaben Shugaban Kasa a 2019 kuwa, Onuesoke ya ce yanzun ba batun da a ke kenan ba, a na kokarin dawo da martabar jam'iyyar ne.

Sai dai kuma ya ce Atiku mutum ne mai gaskiya wanda ba zai yi haufin kallon Buhari cikin kwayan idanu ba fada masa kuskuren sa, ya kuma fada masa cewan ya saki Shugabaancin ko Najeriya ta samu ta cigaba.

Onuesoke ya kuma yi ikirarin Atiku ne sanadin kashi 35 na samun nasarar Buhari a 2015.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel