Nigerian news All categories All tags
Kotu ta yankewa wani maigadi hukuncin zaman gidan yari na wata shida bisa laifin yin barci yayin aiki

Kotu ta yankewa wani maigadi hukuncin zaman gidan yari na wata shida bisa laifin yin barci yayin aiki

- Wata kotun Abuja ta yankewa wani maigadi hukuncin daurin wata 6

- Kotun ta ce ta samu maigadin da laifin sakaci da aiki

- Barayi sun tafka sata yayin da maigadin ke sharar bacci

Wata kotun Abuja dake zaman ta a unguwar Karmo ta aike da wani maigadi ya zuwa gidan yari bisa laifin yin barci yayin aiki.

An gurfanar da Maigadi, Malam Ribado mai shekaru 37, dake zaune a unguwar Jabi bisa tuhumar da laifin sakaci da aiki.

Kotu ta yankewa wanj maigadi hukuncin zaman gidan yari na wata shida bisa laifin yin barci yayin aiki

Kotu ta yankewa wanj maigadi hukuncin zaman gidan yari na wata shida bisa laifin yin barci yayin aiki

Alkalin Kotun, Abubakar Sadia, ya umarci maigadi Ribado da ya biya wanda ya yi karar sa kudi, Naira 363,000, bayan ya amsa laifin sa. Hakazalika alkalin ya yanke masa hukuncin zaman gidan yari na watanni shida ba tare da zabin biyan tara ba. Ya gargadi Maigadin da ya zama mai kyakykyawan hali bayan kammala wa'adin zaman kurkukun.

Tunda fari, 'yar sanda mai gabatar da kara, Florence Auhioboh, ta shaidawa kotun cewar wani mutum ne, Nwankwo Chukwudi, mazaunin Karmo a Abuja, ya shigar da korafi ofishin 'yan sanda dake Utako a ranar 8 ga wannan watan, Disamba.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun gano wata wayar hannu da aka sace daga Najeriya a kasar Indiya

'Yar sandan ta ce me karar ya dauki Malam Ardo aikin gadi ne a shagon sa dake Jabi Forest.

"Maigadin ya yi bacci yayin da ya kamata ya kasance yana saka ido a kan dukiyar da yake gadi, amma sai bacci ya kwashe shi har hakan ya zama silar samun dama wurin barayin da suka shiga shagon suka tafka sata". A cewar 'yar sanda me gabatar da kara.

Hakazalika ta shaidawa kotun cewar barayin sun yi awon gaba da kayan shagon da kudin su ya kai Naira 363,000, kuma duk kokarin jami'an 'yan sanda na gano kayan ya ci tura. Laifin maigadin, a cewar me gabatar da karar, ya saba da sashe na 196 na kundin tsarin fenal kod.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel