Nigerian news All categories All tags
Ai ga irin ta nan: Jam’iyyar PDP ta fara rasa Yankin Yarbawa

Ai ga irin ta nan: Jam’iyyar PDP ta fara rasa Yankin Yarbawa

- Jam’iyyar PDP ta rasa wasu manyan ‘Ya ‘yan ta a Kudu

- Wasu tsofaffin Gwamnonin PDP ne su ka tsere zuwa APC

- Kusoshin APC sun fara cika bakin cewa ta karewa PDP

Mun fahimci cewa Jam’iyyar adawa ta PDP ta fara rasa Yankin Yarbawa bayan babban taron da aka yi na kwanan nan inda Jam’iyyar ta sha kasa wajen zaben Shugabannin ta har ta kai su ka bar wajen taron. Yanzu wasu sun koma APC.

Ai ga irin ta nan: Jam’iyyar PDP ta fara rasa Yankin Yarbawa

Jam’iyyar APC tayi babban kamu a cikin Yarbawa

Idan ku na biye da mu za ku san cewa Jam’iyyar PDP ta rasa wasu manyan ‘Ya ‘yan ta a Kudancin Kasar nan kwanaki. Adebayo Alao-Akala, da tsohon Sanata Teslim Folarin da wasu jiga-jigan PDP ne su ka sauya sheka zuwa Jam’iyyar APC mai mulki.

KU KARANTA: Sabon rikici ya bullo cikin Jam'iyyar PDP

Sauran wadanda su ka koma Jam’iyyar ta APC sun hada da Ayoola Makanjuola, Rasaq Gbadegesin, Rauf Olaniyan da Ambasada Taofeek Arapaja. Kusan dai ba a taba samun lokacin da Jama’a rututu su ka bar Jam'iyyar PDP a lokaci guda irin wannan ba.

Hakan na zuwa ne bayan da Yarbawa da dama su ka fusata da abin da ya faru a PDP inda aka ware su gefe guda wajen zaben shugabanni. Babban jigo a Jam’iyyar APC a Yankin Bola Tinubu yace hakan na nuna cewa ba shakka ta karewa PDP

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel