Nigerian news All categories All tags
An gina wajen sallah a filin wasan Kungiyar Bayern Munich

An gina wajen sallah a filin wasan Kungiyar Bayern Munich

- An gina wajen sallah a filin wasan kwallon Bayern

- Kungiyar ta Jamus ce da wannan namijin kokari

- Akwai Musulmai dai da ke taka leda a fadin Duniya

Mun ji cewa an gina wajen sallah a filin wasan kwallon kafan Kungiyar Bayern Munich na Kasar Jamus kwanan nan bayan da wani daga cikin Musulman ‘Yan wasan Kulob din ya nemi ayi hakan.

An gina wajen sallah a filin wasan Kungiyar Bayern Munich

Wani babban Masallaci a Kasar Jamus

Kamar yadda labari ya zo mana ‘Dan wasan gaban Kungiyar ta Bayern Franck-Bilal Ribery ya kawo wannan shawara wanda ta samu karbuwa a Kungiyar. Kulob din ce dai ta bada kaso mafi tsoka wajen ginin Masallacin.

KU KARANTA: Cristiano Ronaldo ne gwarzon ‘Dan wasan Duniya na bana

Franck Ribery dai Musulmi ne wanda ya taba yin aikin hajji. Yanzu dai Musulmai na iya yin sallah a cikin filin Kulob din na Alianz Arena. Kwanaki dai an gina wajen sallah a St. James Park watau filin wasa na Newcastle.

Kamar dai yadda labari ya zo mana, babban Masallaci aka gina a filin wasan. Wannan ne dai kusan karo na farko da aka taba gina wajen ibada a filin wasa a Kasar ta Jamus inji masana harkar kwallo.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel