Nigerian news All categories All tags
Za’a sake ɗiban wasu sabbin hafsoshin rundunar Yansanda – Gwamnatin tarayya

Za’a sake ɗiban wasu sabbin hafsoshin rundunar Yansanda – Gwamnatin tarayya

Gwamnatin tarayya ta tabbatar ma yan Najeriya zata sake diban wasu sabbin hafsoshin rundunar Yansanda don karfafa tsaro tare da inganta shi a Najeriya, inji rahoton Daily Trust.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya bayyana haka yayin bikin yaye hafsoshin Yansandan Najeiya daya gudana a kwalejin horar da hafsan Yansanda dake garin Jos, inda yace tuni aka tanadi kudaden da za’a kashe wajen diban Yansandan a kasafin kudin 2018.

KU KARANTA: An yi kare jini, biri jini tsakanin Yansandan Najeriya da masu haƙar ma’adanan ƙasa

Majiyar Legit.ng ta ruwaito shugaba Buhari na fadin gwamnatinsa zata tabbatar da inganta walwalar jami’an Yansandan Najeriya ta hanyar kulawa da albashin jami’an da kuma alawus alawus din su.

Za’a sake ɗiban wasu sabbin hafsoshin rundunar Yansanda – Gwamnatin tarayya

Yansanda

Buhari ya bayyana haka ne ta bakin Ministan cikin gida, Abdulrahman Dambazau inda ya ce “Bayan dafe madafan iko, na bada umarnin a diba Yansanda 10,000, don haka nake farin cikin yadda a yau ake yaye hafsoshin Yansanda 767 da kuma wasu Inspektoci a Legas.”

A nasa jawabin, babban sufetan Yansandan Najeriya yace za’a cigaba da diban Yansanda a Najeria don ganin an samu Dansandan guda daya ga mutane 400 a Najeriya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel