Nigerian news All categories All tags
Kowa ya bar gida: An gano ýan Najeriya guda 4,000 dake wani Kurkuku a ƙasar Libya

Kowa ya bar gida: An gano ýan Najeriya guda 4,000 dake wani Kurkuku a ƙasar Libya

Wani dan Najeriya da ya sha da kyar a hannun yan fasa kauri masu siyar da mutane a kasar Libya, Sunday Ehiagwina, ya bayyana cewa a yanzu haka akwai yan Najeriya su 4000 dake garkame a Kurkuku guda daya dake kasar Libya.

Jaridar Punch ta ruwaito Sunday na fadin cewar a baya shi mai hada takalma ne, sai dai bayan kwashe shekaru bakwai yana hada takalma bai ga alamun arziki bane sai ya nemi ficewa zuwa kasar Italiya ta Libya.

KU KARANTA: An yi kare jini, biri jini tsakanin Yansandan Najeriya da masu haƙar ma’adanan ƙasa

Kowa ya bar gida: An gano ýan Najeriya guda 4,000 dake wani Kurkuku a ƙasar Libya

Sunday

Sunday yace a shekarar 2017 ne ya fice daga Najeriya tare da matarsa bayan ya biya wani mutumi mai suna John Osaremwen naira 500,000, inda suka bi ta Kano, Katsina, Nijar har suka isa Libya da isar su ne aka kama su, aka kai su wani sansani, inda sai da ya biya naira 600,000 kafin aka sake shi da matarsa.

Kowa ya bar gida: An gano ýan Najeriya guda 4,000 dake wani Kurkuku a ƙasar Libya

Libya

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Sunday ya cigaba da fadin cewa ya biya wani mutumin kasar Ghana mai suna Prince naira 400,000 don ya haura da su kasar Italiya, inda suka yi ta jira har sai da Yansandan Libya suka kama su, haka zalika yace sun ci duka da cin zarafi, har ma da fyaden mata a Libya.

Daga karshe Sunday yace sakamakon wahalhalun daya sha ba zai kara tunanin barin Najeriya ba, inda yace a yanzu haka akwai yan Najeriya su 4000 dake garkame a Kurkukun Gharyan dake kasar Libya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel