Nigerian news All categories All tags
Osinbajo, Ganduje, Tambuwal, Almakura da Aisha sun shammaci shugaba Buhari

Osinbajo, Ganduje, Tambuwal, Almakura da Aisha sun shammaci shugaba Buhari

Wata tawagar masoya da kuma magoya bayan shugaban kasa Muhammadu Buharia a karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo sun shammaci Buhari a ranar da yake cika shekaru 75 a rayuwa.

Wannan maya da ya samu amincewar Uwargidar shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari ya faru ne a ranar Lahadi 17 ga watan Disamba da daddare, inda Osinbajo ya jagoranci wasu gwamnonin Najeriya, inda suka nemi ganawa da Buhari, sai dai fitowarsa ke da wuya suka fara yi masa wakar zagoyowar ranar haihuwa, wato ‘Happy Birthday to you…..’

KU KARANTA: An yi kare jini, biri jini tsakanin Yansandan Najeriya da masu haƙar ma’adanan ƙasa

Osinbajo, Ganduje, Tambuwal, Almakura da Aisha sun shammaci shugaba Buhari

Murna

Nan take waje ya cika da raha, murna tare da farin ciki, inda aka hangi shugaba Buhari yana ta dariya, da kuma nuna godiyarsa ga masoyan nasa, sa’annan aka yanka ‘Cake’, kamar yadda Legit.ng ta gano.

Osinbajo, Ganduje, Tambuwal, Almakura da Aisha sun shammaci shugaba Buhari

Murna

Cikin tawagar akwai Gwamna Tambuwal, Abdul Aziz Yari, Rochas Okorocha, MA Abubakar, Aregesola, Umar Almakura, Isiaka Ajimobi, Abdullahi Ganduje, Badaru Talamiz, Yahaya Bello, Ibikunle Amosun, Sakataren APC, Mai Mala Bunu da kuma ita kan ta Aisha Buhari.

Osinbajo, Ganduje, Tambuwal, Almakura da Aisha sun shammaci shugaba Buhari

Murna

A wani labarin kuma, shugaba Buhari zai tafi kasar Nijar a ranar Litinin 18 ga watan Disamba don halartar taron cikar kasar Nijar shekar 55 da samun yancin kai.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel