Nigerian news All categories All tags
Manyan abubuwan da ba a raba Shugaba Buhari da su a kullum

Manyan abubuwan da ba a raba Shugaba Buhari da su a kullum

- Shugaban Kasa Buhari ya cika shekaru 75 da haihuwa a yau

- Mun kawo jerin abubuwan da aka san Shugaban Kasar da su

- Kowa dai ya san Buhari bai rabuwa tabarau da kuma hular sa

Yayin da Duniya take taya Shugaban Kasa Buhari murnar zagayowar ranar haihuwar sa. Mun kawo maku jerin wasu manyan abubuwan da ba a raba Shugaba Muhammadu Buhari da su a kullum.

1. Tabarau

Duk wanda ya san Shugaba Buhari to babu shakka ya san shi da tabarau. Kullum dai Shugaban ya kan sa tabaraun da ya saba musamman na Tommy Hilfiger mai tsada.

Manyan abubuwan da ba a raba Shugaba Buhari da su a kullum

Duk wanda ya ga Shugaba Buhari ya ga hula

KU KARANTA: Manyan ‘Yan adawar Buhari sun taya sa murnar cika 75 da haihuwa

2. Hula

Haka kuma a koyaushe ka ga Shugaba Buhari, ko da cikin gona ne, za ka same shi da hula a bisa kan sa. Dama dai an san mutanen Arewa da hula a kai.

Manyan abubuwan da ba a raba Shugaba Buhari da su a kullum

Kowa ya san Shugaba Buhari da karatun jarida

3. Jarida

Haka nan kuma Shugaban Kasar mutum ne mai son karatun jarida da kuma jin labarai. Bini-bini dai za ka ga Shugaban dauke da jaridu yana karantawa ko talabijin.

Bayan nan kuma Shugaba Buhari mutum ne mai yawo da takarda domin rubuta abubuwa da kuma agoga koyaushe a hannun sa kamar yadda ku ka gani.

Manyan abubuwan da ba a raba Shugaba Buhari da su a kullum

Ko me Shugaba Buhari yake rubutawa a littafin sa?

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel