Nigerian news All categories All tags
An hurowa wani Gwamnan APC wuta ya sauka daga kujerar sa

An hurowa wani Gwamnan APC wuta ya sauka daga kujerar sa

- An hurowa Gwamnan Jihar Kogi wuta ya bar kujerar sa

- Hukumar INEC tace Gwamnan yayi rajistar zabe sau 2

- Rajista fiye da sau daya ya saba dokar zabe a Najeriya

Za ku ji cewa ‘Yan adawar Jihar Kogi sun nemi Gwamna Yahaya Bello ya sauka daga mulki bayan Hukumar zabe na Kasa INEC ta same sa da laifin yin rajistar katin zabe fiye da sau daya.

An hurowa wani Gwamnan APC wuta ya sauka daga kujerar sa

An yi kira ga Gwamna Bello ya sauka daga mulki

Hukumar INEC ta tabbatar da cewa Gwamna Yahaya Bello yayi rajista sau 2 wanda ya saba dokar zaben Najeriya. Don haka ne ma ‘Dan Majalisar Jihar James Faleke wanda su kayi takara da Gwamna Bello ya nemi Gwamnan ya sauka daga kujerar.

KU KARANTA: Wani Gwamnan PDP ya samu kan sa cikin babbar matsala

Sanata Dino Melaye wanda su ka dade su na takaddama da Yahaya Bello yace idan har da mutunci ya kamata Bello ya bar mukamin sa bayan an same shi da saba dokar zabe. Shugaban Jam’iyyar PDP a Jihar Prince Bode Ogunmola yace INEC ta wanke su.

Ana dai zargin Gwamnan da rashin biyan albashin ma’aikata da wahalar da Jama’a. Yahaya Bello ya dare mulki ne bayan da ‘Dan takarar lokacin Abubakar Audu ya rasu yana daf da lashe zabe.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel