Gwamnatin tarayya ba zata iya samar da kudin gina hanyoyi ba – Inji ‘yan majalisa

Gwamnatin tarayya ba zata iya samar da kudin gina hanyoyi ba – Inji ‘yan majalisa

- Nauyin gyare-gyaren hanyoyin kasar nan tafi karfin gwamnati kadai

- Shugaban kwamitin majalisar wakilai a kan ayyuka ya ce ‘yan kwangila kawai na bin gwamnati naira tiriliyan 3

- Dan majalisar ya ce ba zai yiwu a ce gwamnati kadai ne zai dauki nauyin gyare-gyaren hanyoyi ba

Shugaban kwamitin majalisar wakilai a kan ayyuka, Toby Okechukwu, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya a halin yanzu 'yan kwangilar gyaran hanya suna bin ta bashin naira tiriliyan 3.

Okechukwu ya kara da cewa akwai wasu nauyin kudade na naira biliyan 300 da ke kan ma'aikatar ayyuka.

Dan majalisar ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a wani taron karshen shekara a Abuja.

Gwamnatin tarayya ba zata iya samar da kudin gyare-gyare hanyoyi ba – Inji ‘yan majalisa

Majalisar wakilai ta tarayya

Legit.ng ta tattara cewa sakamakon bashin, Okechukwu ya ce ba zai yiwu a ce gwamnati kadai ne zai dauki nauyin gina hanyoyi ba.

KU KARANTA: Malabu: Najeriya taci gari, kotun Ingila ta bata gaskiya, za'a dawo da kudin da aka sace

Ya ce: "Ba za mu iya dauka nauyin ayyukan hanyoyin ba, wannan shine gaskiyar magana. Ma’aikatar ayyuka nada bashin naira biliyan 300 a kanta, sa a nan kuma ‘yan kwangila ma na bin naira tiriliyan 3”.

"To, ta yaya za a iya biyan kudin gina hanyoyi? Wannan shine dalilin da ya sa muke kokarin gyara dokar gyare-gyare na hanya wanda zai taimaka mana mu samar da kudaden ta wasu hanyoyi daban-daban, don tallafawa kokarin gwamnatin akan wannan batu. Wannan shi ne abin da sauran kasashen da suka ci gaba suke yi”, inji shi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel