Jam'iyyar PDP ta zargi Buhari da kokarin karkatar da kudaden makamai wajen kamfe din 2019

Jam'iyyar PDP ta zargi Buhari da kokarin karkatar da kudaden makamai wajen kamfe din 2019

Jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) ta bayyana shakkun ta ga wasu makudan kudade da aka ware da suka kai dalar Amurka biliyan 1 don yakar ta'addancin Boko Haram da gwamnatin All Progressives Congress (APC) karkashin jagorancin shugaba Buhari ke shirin yi.

Jam'iyyar ta PDP dai ta bayyana cewa gaskiyar magana ware wadannan kudade cikin sauri da gwamnatin tayi abun a duba ne don kuwa tabbas akwai lauje cikin nadi.

Jam'iyyar PDP ta zargi Buhari da kokarin karkatar da kudaden makamai wajen kamfe din 2019

Jam'iyyar PDP ta zargi Buhari da kokarin karkatar da kudaden makamai wajen kamfe din 2019

Legit.ng ta samu cewa jam'iyyar ta PDP dai ta bayyana ra'ayin nata ne a ta bakin mai magana da yawun ta Kola Ologbondiyan a cikin wata sanarwa inda ya bayyana cewa akwai yiwuwar don zaben 2019 na taho ne shi yasa gwamnatin ta ware kudaden.

A cewar sa bai ga dalilin da za'a ware wadannan makudan kudaden ba domin kashewa ba tare da majalisar tarayya ta amince ba kamar yadda kundin tsarin mulki ya shimfida ba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel