Nigerian news All categories All tags
Rundunar Sojin Najeriya ta damko mutane 400 na Boko Haram da iyalansu a gabar tafkin Chadi

Rundunar Sojin Najeriya ta damko mutane 400 na Boko Haram da iyalansu a gabar tafkin Chadi

Rahotanni daga hukumomin tsaro na dakarun soji sun bayyana cewa, an cafke fiye da mutane 400 na 'yan ta'addan Boko Haram dake bobboye a tsuburai na gabar tafkin Chadi wanda suka hadar da mayakan, matan su da kuma 'ya'yayen su.

A Cikin gudanarwar dakaru ta tsawon makonni biyu a watanni na kwana-kwanan nan an yi nasarar cafke mafi yawan adadi na mayakan Boko Haram a yankunan Arewa maso Gabashin kasar na inji Kanal Onyema Nwachukwu, inda ya ce wannan aiki ya kunshi gudanarwar dakaru ta sama da kasa.

Legit.ng ta ruwaito da sanadin jaridar Kildare Nationalist inda ta bayyana cewa, wadanda aka damko sun hadar da mayakan Boko Haram 167, mata 67 da kuma yara 173. Inda aka mika matan da yara zuwa ga hukumomin sansanan gudun hijira bayan an kammala aiwatar da bincike akan su kamar yadda rudunar sojin ta bayyanar.

Dakarun Soji cikin aiki

Dakarun Soji cikin aiki

Ana ci gaba da zargin Boko Haram da salwantar da rayukan mutane fiye da 20, 000 cikin tsawon shekaru 8 da suka shafe su na addabar kasar nan, wanda ta'addancin na su ya fara ketarawa zuwa kasashe dake makwabtaka da Najeriya, inda ya haifar da munanan matsaloli da suka hadar jefa dubunnan mutane zuwa ga yin gudun hijira da kuma gadar da musu da yunwa.

KARANTA KUMA: Boko Haram: Sarkin Musulmi zai dauki nauyin marayu 200 a jihar Sakkwato

A wannan makon ne gwamnatocin jihohin kasar nan suka yi lamuni ga gwamnatin tarayya wajen ware Dala biliyan 1 domin ci gaba da yakar ta'addanci na Boko Haram, wanda hakan yake nuna sanarwar samun nasara akan su na nan zuwa ba da jimawa ba.

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel