Mummunan rikici ya barke a tsakanin 'yan sanda da masu hakar ma'adanai a Taraba

Mummunan rikici ya barke a tsakanin 'yan sanda da masu hakar ma'adanai a Taraba

Labaran da muke samu daga majiyoyin mu na nuni da cewa kawo yanzu an samu asarar rayuka da dama a wani wurin da ake hakar ma'adanai a tsakanin 'yan kauyen masu hakar da kuma yan sandan Najeriya shiyyar jihar Taraba.

Da yake karin haske game da lamarin, kakakin jami'an yan sandan jihar David Misal, ya bayyana cewa wasu masu hakar ma'adanan ta haramtacciyar hanya a tsawon lokaci mai tsowo ne suka farma jami'an su bayan da gwamnati ta tura su domin tabbatar da bin doka da oda.

Yanzu-Yanzu: Mummunan rikici ya barke a tsakanin 'yan sanda da masu hakar ma'adanai a Taraba

Yanzu-Yanzu: Mummunan rikici ya barke a tsakanin 'yan sanda da masu hakar ma'adanai a Taraba

KU KARANTA: Buhari dan uwa na ne - Atiku

Legit.ng haka zalika ta samu cewa kakakin yan sandan DSP David Misal da ya zanta da majiyar mu ya zayyana cewa a maimakon mutanen su saurari bayani daga 'yan sandan sai suka fara jifa tare da duka, lamarin da ya jawo hargitsi tsakaninsu ke nan.

Sai dai kuma Mista David Misal ya bayyana cewa har yanzu basu gama tattara bayanai ba na game da wadanda suka samu rauni ko jikkata da ma rasa rayuka sakamakon arangamar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel