Tarin bashi dake kaina ne ya sa na ke satan yara domin na warware – Barawon yara a Kebbi

Tarin bashi dake kaina ne ya sa na ke satan yara domin na warware – Barawon yara a Kebbi

Kwamishinan yan sanda na jihar Kebbi, Ibrahim Kabiru ya bayyana cewa sun yi nasarar ceto wasu yara biyu masu shekaru 10 da 11 daga hannun wasu barayin yara a jihar.

A yanzu haka rundunar ta sanar da cewa barayin yaran na garkame a hannunsu.

A cewar Kabiru, masu garkuwan sun bukaci iyayen yaran da su biya zunzurutun kudi har naira miliyan 2.5 kafin su sako su.

Ya kara da cewa sun kama barayin yaran da suka kai 8 ba tare da an biya kudaden fansan su ba a kauyen Dakin Kowa dake karamar hukumar Kontagora jihar Niger.

Kabiru ya ce sun bazama neman yaran ne bayan karan da mahaifin daya daga cikin yaran mai suna Christopher Nnagbo ya kai ofishin su ranar 5 ga watan Disamba.

KU KARANTA KUMA: Zahra Buhari da mijinta sun cika shekara daya da aure

Kabiru ya ce yanzu haka Christopher ya karbi dan sa sannan suna neman iyayen daya yaron da suka kwato tare da dan Christopher din.

Ya kuma yi kira kira ga mutane da su guji karban bashin da ya sha karfin su musamman yadda shugaban barayin yaran ya furta cewa ya fara wannan sa’a ce don ya sami kudin biyan wata bashin da ya ci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel