Nigerian news All categories All tags
Muna bukatar dakarun sojin mu a gida – Buhari ya fada ma Guinea Bissau

Muna bukatar dakarun sojin mu a gida – Buhari ya fada ma Guinea Bissau

Shugaban kasa ya gana da shugaban kungiyar kasashen Afrika Marcel A. de Souza, a fadar shugaban kasa dake babban birnin tarayya Abuja, a yau Juma’a, 15 ga watan Disamba.

Shugabannin guda biyu sun tattauna wasu muhimman abubuwa wanda zai kawo ci gaba a nahiyar Afrika.

Shugaba Buhari ya bayyana fatan cewa hukumomin Guinea Bissau zata yarda da hanyar tsarin mulki wajen sasanta rikici dake kasar.

Yace Najeriya ta bukaci rundunarta dake aikin tabbatar da zaman lafiya da su dawo gida.

Hakan na kunshe ne a cikin wani jawabi daga mai magana da yawun shugaban kasa, Mallam Garba Shehu yayinda ya tarbi shugaban hukumar ECOWAS, Marcel A. de Souza, a fadar shugaban kasa, a Abuja.

Muna bukatar dakarun sojin mu a gida – Buhari ya fada ma Guinea Bissau

Muna bukatar dakarun sojin mu a gida – Buhari ya fada ma Guinea Bissau

An rahoto bayanin Buhari inda yake cewa yana zaton samun rahoto kan al’amarin Guinea Bissau a taron tattaunawa karo na 52 na hukumar ECOWAS na shuwagabannin da gwamnatoci da za a gudanar a ranar Asabar a Abuja.

KU KARANTA KUMA: NDA ta dauki dalibai 360 a fannin karatun digiri daban-daban (hotuna)

Shugaban yace “Muna bukatar sojojinmu a gida, kuma ina fatan shugaban kasar zai amince da hanya da yazo a tsarin mulki wajen magance al’amarin”.

Muna bukatar dakarun sojin mu a gida – Buhari ya fada ma Guinea Bissau

Muna bukatar dakarun sojin mu a gida – Buhari ya fada ma Guinea Bissau

Buhari ya kara da cewa abun murna ne cewa hukumar ta bukaci gaskiya daga ma’aikatun hedikwatan ta, wanda hakan ne yasa ta gayyaci hukumar EFCC daga Najeriya don bincikar takardunta.

Muna bukatar dakarun sojin mu a gida – Buhari ya fada ma Guinea Bissau

Muna bukatar dakarun sojin mu a gida – Buhari ya fada ma Guinea Bissau

Shugaba Buhari yace “Godiya kan tabbatar da hakan, kuma ga nuna gaskiya a hedikwatan hukumar ECOWAS,” ya kara da cewa Najeriya zata cigaba da cika alkawaarin ta ga yankin hukumar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel