Nigerian news All categories All tags
NDA ta dauki dalibai 360 a fannin karatun digiri daban-daban (hotuna)

NDA ta dauki dalibai 360 a fannin karatun digiri daban-daban (hotuna)

Makarantar Sojojin Najeriya ta dauki dalibai 360 a karo na 69 a fanni daban-daban na karatun digiri.

Daliban wadanda aka kwasa kwanan nan don fara karatu a makarantar zasu gudanar da karatun digiria bangarori daban-daban a fadin sashen makarantar guda hudu da ake dasu a makarantar sojojin Najeriya, wadanda suka hada da sashen al’adu da zamantakewar kimiyya (Faculty of Arts and Social Sciences), sashen koyon karatun injiniya (Faculty of Engineering), sashen Kimiyya (Faculty of Science) da kuma sabuwar sashe da aka kirkiro na Kimiyyar sojoji da karatun da’a (Military Science and Interdisciplinary Studies).

NDA ta dauki dalibai 360 a fannin karatun digiri daban-daban (hotuna)

NDA ta dauki dalibai 360 a fannin karatun digiri daban-daban

Yayinda yake jawabi ga sabbin daliban, babban bako a wajen taron, Birgediya Janar JN Temlong (mai ritaya), ya taya daliban murna kan dama da suka samu na shiga makarantar.

Ya bukacesu da su jajirce akan karatunsu, su kuma dace da junansu a gwagwarmayar su na neman ilimi zuwa lokacin kammalawa.

NDA ta dauki dalibai 360 a fannin karatun digiri daban-daban (hotuna)

NDA ta dauki dalibai 360 a fannin karatun digiri daban-daban

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya zata kara albashin ma’aikata a shekara mai zuwa – Ministan kwadago ya bad a tabbaci

Janar Temlong ya ci gaba da kalubalantar daliban da su kasance masu kirkira da jajircewa yayinda suke karatun su na aikin sojoji.

NDA ta dauki dalibai 360 a fannin karatun digiri daban-daban (hotuna)

NDA ta dauki dalibai 360 a fannin karatun digiri daban-daban

Taron wanda aka rantsar da daliban 69RC ya samu halartan manyan ma’aikatan makarantar, mambobin makarantar da baki daga waje.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel