Nigerian news All categories All tags
Kachikwu ya gabatar wa majalisar zartarwa kwangilar da ya zargi Baru ya bayar a bayansa

Kachikwu ya gabatar wa majalisar zartarwa kwangilar da ya zargi Baru ya bayar a bayansa

- Dr. Ibe Kachikwu ya gabatar wa majalisar zartarwa kwangilar da ya zargi Baru ya bayar a baya

- Majalisar zartarwa ta amince da aikin kwangilar gina bututun mai da aka ta cece-ku-ce akai a baya

- Kwangilar ta kunshi har da aikin dasa bututun gas wanda zai tashi daga Ajaokuta ta hada Kaduna da kuma Kano

Karamin ministan albarkatun man fetur ta kasa, Dr. Ibe Kachikwu, ya nema amincewar majalisar zartarwa akan gudanar da kwangilar da a wasu watannin baya ya zargi babban daraktan kamfanin NNPC, Maikanti Baru ya bayar a bayansa.

Ministan ya bayyana wa manema labarai da ke fadar gwamnati a Aso Rock cewa majalisar ta amince da aikin kwangilar gina bututun mai wadda a baya ya bayyana cewa Baru ya bayar ga wani kamfanin kasar Sin.

Wannan kwangilar da majalisar amince ta kunshi har da aikin dasa bututun gas da za a yi na hadin-guiwa, wanda zai tashi daga Ajaokuta ta hada Kaduna da kuma Kano.

Kachikwu ya gabatar wa majalisar zartarwa kwangilar da ya zargi Baru ya bayar a bayansa

Karamin ministan albarkatun man fetur, Ibe Kachikwu da shugaba Muhammadu Buhari

Idan dai baku manta ba, Legit.ng ta ruwaito a baya irin cece-ku-ce da aka yi akan wannan kwangilar a wasu watannin da suka gabata, inda Kachikwu ya yi zargin cewa Baru ya zaga baya ya bayar da kwangilar ba tare da sanin sa ba.

KU KARANTA: Yau kuma: Sanata David Mark ya shiga hannun Hukumar EFCC

Amma kuma sai ga shi a ranar Laraba, 13 ga watan Disamba, ministan ya ce ya maido kwangilar ne domin ta samu amincewar majalisar Zartarwa, kamar yadda tun da farko ya kamata a yi.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel