Man fetur zai wadata cikin kwanaki 2, Inji Kachikwu

Man fetur zai wadata cikin kwanaki 2, Inji Kachikwu

- Karamin ministan man fetur ya bada tabbacin kawo karshen karancin man fetur a dukkan sassan kasar nan cikin kwanaki 2

- Ministan ya fadi hakan lokacin da yake jawabi a taron tattalin arziki na kasa da a ka yi ranar Alhamis

- Ministan yace Najeriya tana da ajiyar man fetur da za'a fito dashi kuma za'a rabar zuwa duka sassan kasar nan kafin makon mai zuwa

Karamin ministan man fetur, Ibe Kachikwu ya baiwa gwamnoni 36 na jihohin Najeriya tabbacin cewa karancinman fetur da a ke fama dashi zai gushe cikin kwanaki 2.

Mista Kachikwu ya bada wannan tabbacin ne a lokacin da yake jawabin ga gwamnonin da ministoci da suka halarci taron tattalin arzikin na kasa da a ka gudanar ranar Alhamis.

Man fetur zai wadata cikin sa'o'i 48, Inji Kachikwu

Man fetur zai wadata cikin sa'o'i 48, Inji Kachikwu

A yayin da yake jawabi ga manema labarai a gidan gwamnati, Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki yace karamin ministan albarkatun man fetur ya basu tabbacin cewa wahalar man fetur da a ke fama dashi a sassan kasar nan zai gushe cikin kwanaki biyu.

DUBA WANNAN: Trela dauke da buhunan shinkafa ta fada wani gida, ta kashe jariri da wasu mutane

Saboda akwai man fetur a gangar ajiya da za'a fitar domin rabawa ga Jihohin Najeriya, Ministan yace man fetur din zai isa dukkan lunguna da sakuna cikin kwanaki 2. Karamin ministan ya kara jadada ma mahalarta taron FEC a ranar Laraba cewa karancin man fetur din zai kare kafin makon da za'a shiga.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel