Nigerian news All categories All tags
Dalilin da yasa kotu ta hana bayar da belin Maryam Sanda a karo na biyu

Dalilin da yasa kotu ta hana bayar da belin Maryam Sanda a karo na biyu

Babbar kotun kasa dake birnin tarayya Abuja ta sake kekashewa akan bayar da belin Maryam Sanda, matar da ta kashe mijinta a sakamakon rashin kwakkwaran dalilai da lauyoyin ta suka gaza baiwa kotun.

Maryam wadda 'ya ce ga Maimuna Aliyu, tsohuwar shugaban bankin Aso Saving, 'yan sanda sun yi caraf da ita sakamakon kashe mijinta Bilyaminu, wanda da ne ga tsohon shugaban jam'iyyar PDP, Mohammed Bello.

Rahotanni sun bayyana cewa, Maryam ta dabawa mijin ta kaifi a gidan su dake gundumar Maitama ta Abuja makonni kadan da suka gaba a sakamakon tuhumuar sa da take yi da keta mata haddi na aure.

A makonnin da suka gabata, wannan babbar kotun ta kekashe akan bayar da belin ta wanda ta sake maimaita hakan a karo na biyu a ranar Alhamis din da ta gabata, inda alkali mai shari'a Halilu yace, zai yi nazari cikin shaidar rashin lafiya ta lauyan ta Mista Joseph Dauda ya gabatar domin neman belin wadda yake karewa.

Maryam Sanda tare da gandireba

Maryam Sanda tare da gandireba

Alkalin ya bayyana cewa, babu wata hujja da doka ta tanadar akan cewa wannan rashin lafiya da Maryam ke fama da ita ba za a iya kulawa da ita ba a yayin da take tsare. Inda ya kuma ce, kasancewar ta mai shayarwa ba hujja ba ce ta bayar da belin ta.

KARANTA KUMA: Wani harin kunar bakin-wake ya shekar da jami'an 'yan sanda 13 a kasar Somalia

Sai alkalin ya bayar da belin mahaifiyar Maryam da dan uwanta wanda su ma ake tuhumar su da hannu wajen aikata laifin, tare da bayar da sharadi na gabatar da mutane biyu na kowanen su da zasu tsaya musu a matsayin jingina kuma su kasance mazauna tantagwaryar birnin na tarayya.

Ya kuma bukace su da su baiwa kotu shaidar su ta tafiye-tafiye da fasfo tare da neman majinginan su da bayar da shaidar ta kadarori da suke da ita a Abuja, inda ya daga sauraron karar zuwa ranakun 5, 6 da kuma 7 na watan Fabrairun shekarar 2018.

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel