Nigerian news All categories All tags
Kotun koli ta koka a kan yawaitar keta hakkin yara sassan kasar nan

Kotun koli ta koka a kan yawaitar keta hakkin yara sassan kasar nan

- Shugaban kotun kolin Najeriya ya nuna damuwar sa kan yadda keta hakkin yara ke yawaita a kasar nan

- Yayi fadi wannan ne a jawabin da yayi wajen bude taron Alkalan Najeriya da Cibiyar nazarin shari'ar musulunci ta shirya

- Manufan taron shine tattaunawa domin lalubo hanyoyin da za'a bi domin magance matsalar

Shugaban kotun kolin Najeriya, Alkali Ibrahim Tanko Muhammad ya jawo hankalin al'umma a kan yadda ake keta hakkin yara kanana a wurare daban daban a fadin kasar nan.

A jawabin da yayi na bude taron shekara-shekara na Alkalan Najeriya da Cibiyar Nazarin Sharia'ar Musulunci ta dauki nauyi da aka gudanar a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, Muhammad yace keta hakkin yara ya zama ruwan dare, hakan yasa dole ayi kokarin kawar da shi.

Kotun koli ta koka ga yawaitar keta hakin yara sassan kasar nan

Kotun koli ta koka ga yawaitar keta hakin yara sassan kasar nan

Justice Muhammad wanda ya samu wakilcin Justice Ahmad Belgore yace faduwa ne tazo daidai da zama kasancewar taken taron na bana shine "Rawar da kotunan Shariah ke takawa wajen bin hakkin yaran da aka zalunta"

DUBA WANNAN: Labari da duminsa: Gwamnoni sun amince a ware dala biliyan 1 daga asusun rarar man fetur domin yakar ta'addanci

Ya kuma yi kira da masu ruwa da tsaki a fanin su baiwa Cibiyar Nazirin Shari'ar Musuluncin tallafi da kwarin gwiwa domin ta cigaba da ilmantar da Alkalai, lauyoyi da sauran masu aiki a fanin ta shariar ta musulunci.

Shugaban Jami'ar ta ABU, Farfesa Ibrahim Garba yace bayan tattauna kan kare hakkin yaran, zasu tattauna a kan matsaloli da suka hada da mulki da kuma rabon gado.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel