Gwamnoni basa bawa shugaba Buhari hadin kai a yakin da yake yi da cin hanci - Jigo a jam'iyyar APC

Gwamnoni basa bawa shugaba Buhari hadin kai a yakin da yake yi da cin hanci - Jigo a jam'iyyar APC

- Farfesa Richard king ya ce gwamnonin kasar nan na bata yaki da cin hanci da shugaba Buhari ke yi

- Basa bawa shugaba Buhari hadin kan da ya kamata wajen yaki da cin hanci

- Farfesa King jigo ne a jam'iyyar APC mai mulki

Wani jigo a jam'iyyar APC mai mulki, Farfesa Richard King, ya bayyana cewar gwamnonin kasar nan basa bawa shugaba Buhari hadin kan da ya kamata wajen yaki da cin hanci.

Farfesa King ya fadi haka ne a wata hira da yayi da kamfanin jaridar "The Nation".

Gwamnoni basa bawa shugaba Buhari hadin kai a yakin da yake yi da cin hanci - Jigo a jam'iyyar APC

Farfesa Richard King, Jigo a jam'iyyar APC

Da yake amsar tambayar ko ya ya yake ganin kokarin gwamnatin tarayya a bangaren yaki da cin hanci?, Farfesa King ya ce "Gwamnatin tarayya tana yaki da cin hanci yadda ya kamata, babu tantama a kan hakan. Ya kamata a ce yaki da cin hancin ya ratsa har cikin jihohin kasar nan, domin har yanzu iya Abuja yaki da cin hancin ya tsaya. Yaki da cin hanci bai kamata ya zama aikin gwamnatin tarayya ko jam'iyyar APC kawai ba. Aiki ne da ya shafi gwamnatoci da jam'iyyu a dukkan matakai".

DUBA WANNAN: Watanni 14 kafin zaben 2019: Ku sadu da dan siyasar da kan iya maye gurbin Osinbajo da dalilin yin hakan

Da aka sake tambayar Farfesa King, ko babu laifi idan aka ce gwamnoni na dakile yaki da cin hanci?, sai ya kada baki ya ce "Ko kadan babu laifi a fadin hakan. Na san gwamnan da yake ta kokarin hana hukumar EFCC aikin ta a jihar sa. Ko kadan bai dace ace gwamna zai aikata hakan ba koda kuwa zargin aikata cin hancin kawai hukumar ke bincika. Hana hukumar EFCC ta yi aikin ta, tamkar hana jam'ian 'yan sanda binciken wanda ake zargi da aikata laifi ne. Kamar, misali, a jiha ta, Akwa Ibom, gwamnatin jihar har kotu ta shigar da karar hukumar EFCC domin a hana hukumar binciken asusun jihar. Yin hakan daidai yake da daurewa cin hanci gindi. Idan har gwamnonin nada tsarki me zai saka su adawa da aikin hukumar EFCC?".

Ko a lokacin da shugaba Buhari ya kai ziyara Kano, saida ya koka cewar yaki da cin hanci ne yafi wahalar da shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel