Nigerian news All categories All tags
Shugaba Buhari zai kaddamar da gagarumin tashar makamashin gas a yankin Arewacin kasar

Shugaba Buhari zai kaddamar da gagarumin tashar makamashin gas a yankin Arewacin kasar

Rahotanni sun kawo cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari na shirin kaddamar da wata tashar makamashin gas a yankin Arewacin Najeriya.

Wannan tasha na gas zai wanzu zuwa sassa daban-daban. Zai kuma taimaka matuka wajen kawo karshen rashin wutar lantarki ciki harda samar da ayyukan yi, da habbaka tattalin arzikin kasar.

Har ila yau hakan zai sa kasashen ketare kamar su China da sauransu su rika rige-rigen zuwa arewacin kasar domin kafa jari sakamakon yunkurin kafa wata makekiyar tashar makamashin gas a Ajakuta, inda za a shinfida bututai daga Ajakutan zuwa sassan arewacin Najeriya musamman ma Abuja da Kaduna da Kano.

Shugaba Buhari zai kaddamar da gagarumin tashar makamashin gas a yankin Arewacin kasar

Shugaba Buhari zai kaddamar da gagarumin tashar makamashin gas a yankin Arewacin kasar

Sannu a hankali bututan za su isa wurare da dama na arewacin kasar.

KU KARANTA KUMA: Jiragen ruwa 9 cike da man fetur da sauran kayayyaki sun isa tashar jirgin Lagas

Kafa wannan tashar, zai ci kimanin dalar Amurka Miliyan dubu dari biyu ($200,000m)

Kakakin shugaban kasa, Garba Shehu ya ce manyan kamfanoni su ma za su saka jari ciki ta yadda za a gudanar da tashar makamashin ba tare da cikakkiyar sa hannun gwamnati ba saboda a kula da tashar.

Ya bayyana cewa muddun mutane su ka saka jari ciki to ba za su yadda a barnata wurin ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel