Nigerian news All categories All tags
An gurfanar da Maryam Sanda, mahaifiyarta da dan uwanta kan zargin kashe da tsohon shugaban PDP

An gurfanar da Maryam Sanda, mahaifiyarta da dan uwanta kan zargin kashe da tsohon shugaban PDP

Rundunar yan sanda a ranar Alhamis ta gurfanar da Maryam Sanda, Mahaifiyarta, Maimuna Aliyu; kaninta, Aliyu Sanda; da wacce ake tuhuma ta hudu, Sadiya Aminu da zargin kisan kai.

Misis Sanda ta kasance suruka ga tsohon shugaban jam’iyyar PDP Mohammed Bello. An zargeta da kashe mijinta, Biliyaminu Bello, bisa zargin rashin aminci.

Shekarunsu biyu da aure, kafin aukuwar al’amarin a watan Nuwamba.

An gurfanar da Maryam Sanda, mahaifiyarta da dan uwanta kan zargin kashe da tsohon shugaban PDP

An gurfanar da Maryam Sanda, mahaifiyarta da dan uwanta kan zargin kashe da tsohon shugaban PDP

A ranar Alhamis, 14 ga watan Disamba an gurfanar da Misis Sanda, da mahaifiyarta Maimuna, wacce ke fuskantar laifin zamba, tare da sauran mutane biyu a kotu.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya sha ruwan yabo daga yan Najeriya da suka amfana da shirin N-Power

A cewar sabon zargin, an zargi wadanda ake tuhuma din da laifin kisan kai da kuma take gaskiya.

Misis Sanda ta kasance lullube da mayafi yayinda ta dukar da kanta kasa a lokacin da ake karanto tuhumar da ake yi a kansu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel