'Yan sandan SARS sun yi awon gaba da wani dan kasuwa bayan sun harbe shi a kugu

'Yan sandan SARS sun yi awon gaba da wani dan kasuwa bayan sun harbe shi a kugu

- Sun tare kasuwar ne bayan a hanyar sa ta komawa gida bayan tashi daga kasuwa

- 'Yan sandan na cikin fararen kaya

- Sun yi harbin iska domin firgita mutanen da suka yi yunkurin dakatar da su

Iyalin wani dan kasuwar kayan wutar lantarki ta Alaba dake Lagos sun shiga cikin dimuwa bayan da suka ce jami'an SARS sun harbi dan uwan su kuma sun yi awon gaba da shi ya zuwa wani wurin da basu sani ba.

'Yan sandan SARS sun yi awon gaba da wani dan kasuwa bayan sun harbe shi a kugu

'Yan sandan SARS sun yi awon gaba da wani dan kasuwa bayan sun harbe shi a kugu

Dan kasuwar, Eche Israel, mai shekaru 30, ya gamu da wannan danyen aiki na jami'an SARS a hanyar sa ta komawa gida a kan babur din kabu-kabu, bayan ya tashi daga kasuwa. Jami'an na SARS, dake cikin fararen kaya, sun dakatar da shi a daidai mile 2, amma sai ya bukaci ya san dalilin tsayar da shi, bayan sun yi cacar baki sai jami'an suka sallami dan acabar da ya dauko shi sannan suka harbe shi a kugu.

Jami'an sun yi harbin iska domin tarwatsa jama'ar da suka fara taruwa domin ganewa idon su tare da yunkurin dakatar da su, sannan suka saka shi cikin bayan wata mota suka tafi da shi.

'Yar uwa ga Eche ta ce wani makobcin su da abin ya faru a kan idon sa ne ya sanar da su abinda yake faruwa. Sannan ta kara da cewar dan uwan na ta na sayar da kayan wutar lantarki ne a kasuwar Alaba kuma yana hanyar dawowa gida ne wannan tsautsayi ya faru da shi.

DUBA WANNAN: Hukumar 'yan sandan Najeriya ta garkame jami'an SARS 32

"Dan kasuwa ne, ba dan fashi ba ne, basu samu komai a tare da shi ba bayan wayar sa ta hannu da kudin ciniki, amma haka siddan suka harbe shi a kugu kuma suka wulla shi cikin bayan mota suka tafi da shi wurin da har yanzu bamu sani ba, domin duk ofisoshin 'yan sandan da muka ziyarta sun ce babu wani mai suna Eche cikin wadanda suke tsare da su". Inji Mary, 'yar uwa ga Eche.

Da aka tuntubi kakakin hukumar 'yan sanda na jihar Legas, SP Chike Oti, ya ce zai waiwayi majiyar mu, amma har yanzu shiru.

Jami'an SARS dai sunyi kaurin suna wajen yin dirar mikiya a kan mutanen da ake zargi da aikata laifi, dalilin dake jawo yawaitar samun korafe-korafen cin zarafin bil'adama daga bangaren jami'an.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel