Nigerian news All categories All tags
Wani ma'aikacin gwamnati zai mika ababen hawa 86 da gidaje 4 ga gwamnatin tarayya

Wani ma'aikacin gwamnati zai mika ababen hawa 86 da gidaje 4 ga gwamnatin tarayya

- Ma'aikacin ya mallaki motoci 86, da gidaje 4 da wasu dimbin kadarori daga 2016 zuwa 2017

- Ya kuma gaza bayyana yadda ya tara wannan dimbin dukiya da albashin da bai kai N500,000 ba a wata

- Don haka ne kotu ta umurci ya mika su hannun gwamnatin tarayya har zuwa a kammala bincike

Wata babbar kotu a Abuja ta umurci wani ma'aikacin gwamnati da ya mika gidajen sa guda 4, motoci 4, kamfanin haki da kuma kwantena guda 8 zuwa hannun gwamnatin tarayya. An ba shi wannan umurni ne sakamakon bincike da gwamnati ke yi game da yadda ya tara wadannan kadarori.

Wani ma'aikacin gwamnati zai mika ababen hawa 86 da gidaje 4 ga gwamnatin tarayya

Wani ma'aikacin gwamnati zai mika ababen hawa 86 da gidaje 4 ga gwamnatin tarayya

Ma'akacin mai suna Ibrahim Tumsah, wanda shi ne Daraktan Shige da Ficen kudi a Ma'aikatar Wutan Lantarki da ayyuka da Muhalli, ya na da albashin da bai kai N500,000 ba a wata, amma ya iya mallakan wadannan kadarori daga 2016 zuwa 2017.

DUBA WANNAN: Wasu ma'aikatan hukumar lantarki sun sha cizo da duka a hannun wata mata

Bincike ya nuna cewan Ibrahim ya mallaki kadarorin ne da sunan kamfanoni guda biyu da ya masu rajista da gwamnati. Ya kuma sanya dan uwan sa Tijjani Tumsah wanda ba shi da wata sana'a ballantana aikin gwamnati, a matsayin Manaja mai gudanar da kamfanonin.

Koda suka bayyana a gaban kwamitin bincike, sun gaza amsa yadda su ka tara wannan dukiya mai dimbin yawa. Sannan kuma ba su san iya adadin asusun bankunan da su ke da su ba. Dama dai an sha zargin Ibrahim da rashawa da kuma keta alfarmat aikin sa.

Motocin duk masu tsada ne, duk ciki babu na banza. Sannan kwantena 7 cikin 8 shake su ke da kayaki masu tsadan gaske. A halin yanzun dai kotu ta umurci kwamktin binciken da ta kammala binciken ta nan da watanni 3. Don haka ta daga sauraren karan har zuwa 6 ga watan Mayu na 2018.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel