Nigerian news All categories All tags
Na yi na’am da Buhari da Osinbajo 100 bisa 100 Inji Bola Tinubu

Na yi na’am da Buhari da Osinbajo 100 bisa 100 Inji Bola Tinubu

- Asiwaju Bola Tinubu ya yarda da kamun ludayin Osinbajo

- Yace da shi da Yarbawa duk su na tare da Buhari da Osinbajo

- Tinubu yace ba shi da niyyar zama Mataimakin Buhari a 2019

Ofishin Bola Tinubu ya karyata rade-radin Jaridar The Sun na cewa yana neman maye gurbin Osinbajo. Tinubu yace ko a 2015 Buhari yayi masa wannan tayi amma ya mika Yemi Osinbajo. Tinubu ya ma yabawa aikin Gwamnatin Buhari.

Na yi na’am da Buhari da Osinbajo 100 bisa 100 Inji Bola Tinubu

Tinubu yace a 2015 Buhari yayi masa tayin Mataimakin Shugaban Kasa

Jiya mu ka ji cewa tsohon Gwamnan Legas kuma babban jigo a Jam’iyyar APC mai mulki Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yace yayi amanna da irin kamun ludayin Mataimakin Shugaban Kasa Farfesa Yemi Osinbajo inda yake raddi ga wani rahoto.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari za ta kammala wasu hanyoyin jirgin kasa

Bola Tinubu ya karyata cewa yana kokarin maye gurbin Osinbajo watau ya zama Mataimakin Shugaba Buhari a zaben 2019. Babban ‘Dan siyasar Kasar yace wannan karyar banza ce yayin da Gwamnatin ba ta wuce shekaru 2 da rabi da kafuwa ba.

Tinubu ya yabawa mulkin na Buhari da Osinbajo inda yace a yanzu Gwamnati ta rike amanar dukiyar al’umma da kuma rayukan su, sannan kuma ana kokarin farfado da tattalin arzikin Kasar. Yace da shi da Yarbawa su na bayan Gwamnatin nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel