Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

- An fara samun sauki a gidajen man fetur da ke birnin tarayya, Abuja

- A wasu gidajen man motoci basu wuce 2 ko 3 a bakin famfo ba

- Manajan gidan man na A. Y. M Shafa ya ce suna sayar da lita naira 145 maimakin 143 da suka saba a baya

Wani wakilin jaridar NAN, majiyar Legit.ng wanda ke tare da tawagar masu sa ido na NNPC da jami'an PPMC a wasu gidajen man a babban birnin tarayya a ranar Laraba, 13 ga watan Disamba sun lura cewa, yayin da layin masu bukatar saya man ta ragu a wasu gidajen man, wasu motoci kuma shiga da fice suke yi a wasu wurare saboda babu layin gaba daya.

A gidan mai na Total a Zone 1, Wuse, tawagar sun lura cewa an sauke tankar man fetur kuma mai gidan man, Mista Patrick Okogo, ya shaida wa 'yan jaridu cewa kodayake akwai layi, amma akwai man da dama.

A gidan man na Oando wanda ke Mabushi a Abuja, motoci guda 2 zuwa 3 ne ke bakin kowane famfo man.

Layin man fetur da ta kuno kai a Abuja ta fara raguwa sosai a halin yanzu

Layin saya man fetur

Lokacin da tawagar NNPC / PPMC ta isa gidan man na A. Y. M Shafa, akwai tsararraki, ba kamar yadda ya kasance kwanan baya ba.

KU KARANTA: 2019: Ya yi mun gani, ba zamu wahala wajen tallata Buhari ba – Gwamnan jihar Nassarawa

Mai kula da gidan man, Abdullahi Sambo, ya shaida wa manema labarai cewa "Muna da lita miliyan 200 na man fetur wanda zai iya kwana uku. Ba mu sayar wa masu galon”.

"Haka ne, muna sayarwa a kan naira 143 a kowace lita, amma yanzu umarnin daga hedkwatar ya sanya mu sayar naira 145. Muna fatan zamu koma farashinmu na farko idan muka samo isashen man".

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel