Ta'addanci: Sojojin Najeriya suna fafatawa da mayakan Boko Haram a Mainok yanzu haka

Ta'addanci: Sojojin Najeriya suna fafatawa da mayakan Boko Haram a Mainok yanzu haka

- Sojojin Najeriya suna fafatawa da mayakan Boko Haram a Mainok a yanzu haka

- Kauyen Mainok yana kimani kilomita 58 daga Maiduguri, birnin jihar Borno

- Mayakan sun shigo kauyen ne daga cikin daji da ta hade Mainok tare da Buniyadi na jihar Yobe

Rahoton da muka samu daga jaridar PREMIUM TIMES ta nuna cewa sojojin Najeriya suna nan yanzu suna fafata don fatataki harin miyagu mayakan kungiyar Boko Haram wadanda suka kai harin ta’addanci a kauyen Mainok, yankin karamar hukumar Kaga na jihar Borno.

Kauyen Mainok yana kimani kilomita 58 daga Maiduguri, birnin jihar Borno.

Wani jami'in tsaro a jihar Borno ya tabbatar wa majiyar Legit.ng cewa ‘yan kuna bakin waken da suka kai hari sun shigo ne daga cikin daji da ta hade Mainok tare da Buniyadi na jihar Yobe.

Ta'addanci: Sojojin Najeriya suna fafatawa da mayakan Boko Haram a Mainok yanzu

Sojojin Najeriya

"Sojojinmu suna fafatawa da wadanda suka kai harin a yanzu haka kamar yadda muka ji", in ji wanda ya ce ba zai ambaci sunansa ba don dalilai na tsaro.

KU KARANTA: Kwararrun ma'aikata na musamman na Sufeto Janar sun cafke miyagu 5 a garin Aba

Al’ummar garin sun kasance daga cikin ‘yan gudun hijira na farko da aka mai da su gida a farkon wannan shekarar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel