Nigerian news All categories All tags
Kaduna: El-rufai ya shigar da kara akan wani tsohon jigon APC, ya bukaci diya biliyan 1

Kaduna: El-rufai ya shigar da kara akan wani tsohon jigon APC, ya bukaci diya biliyan 1

- Gwamnan Kaduna ya kai karar Datti Baba-Ahmed tsohon jigo a jam’iyyar APC a kotu

- Gwamnan na zargin Baba-Ahmed da laifin lalata masa suna

- Baba-Ahmed ya zargi gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari da cin hanci

Kwanaki bayan ficewa daga jam’iyya da ke mulki, APC, gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai ya kai karar tsohon jigo a jam’iyyar, Datti Baba-Ahmed a kotu.

Gwamnan ya kai karar Baba-Ahmed ne akan zargin lalata masa suna kuma ya bukaci a biya sa kudin diya na naira biliyan 1.

Koda yake ba a bayyana cikakkun bayanai game da karar ba a lokacin wannan rahoton, gwamnan, da kansa ya tafi babban kotun jihar don shigar da karar da aka yi wa Baba-Ahmed akan lalata masa suna.

Kaduna: El-rufai ya shigar da kara akan wani tsohon jigon APC, inda ya bukaci diya biliyan 1

Gwamna Nasir El-Rufai a kotu

Malam El-Rufai ya yi ikirarin a biya sa naira biliyan 1 a matsayin kudin diya kamar yadda aka wallafa a shafukan sada shumunta ta twitter na gwamnatin jihar.

KU KARANTA: Farfaɗo da martabar Arewa: Muhimman matakai guda 10 da ya dace yan Arewa su ɗauka – Shehu Sani

Idan dai baku manta ba Legit.ng ta ruwaito yadda Datti Baba-Ahmed ya bar APC bayan ya zargi gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari akan kasawa da cin hanci.

Baba-Ahmed, wanda ya kasance dan majalisar wakilai daga 2003 zuwa 2007 da kuma sanata a karkashin jam’iyyar CPC a shekara ta 2011, ya ce ya koma babban jam’iyyar adawa ta PDP.

"An kafa gwamnatin shugaba Buhari ne da kudaden sata kuma kashi 80 daga 100 ta fito daga PDP, abin da yake kira yaki da cin hanci da rashawa ba gaskiya bane", in ji Baba-Ahmed.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel