Hukumar jin dadin Alhazai zata mayarwa da alhazan jihar Kaduna kudaden su na shekarun baya

Hukumar jin dadin Alhazai zata mayarwa da alhazan jihar Kaduna kudaden su na shekarun baya

Hukumar jin dadin Alhazai reshen jihar Kaduna ta bayar da sanarwar cewa, zata fara mayarwa da alhazai kudaden su na shekarun 2016 da 2017 a mako mai gabatowa sakamakon malalo kudi na naira miliyan 129 da hukumar ta kasa baki daya tayi.

Shugaban reshen, Mallam Imam Hussaini Tsoho, shine ya bayyana wa manema labarai a ranar Larabar da ta gabata inda yace, za a kasafta wannan adadin kudi ga alhazai na shekarun 2016 da kuma 2017.

Aikin Hajji

Aikin Hajji

A sakamakon alhazai da basu samu damar gudanar da aikin hajjin su ba a shekarun da sanadiyar rashin lafiya, juna biyu ko kuma wasu dalilai, shi ya sanya hukumar ta dauki alhakin maya musu da kudaden su.

KARANTA KUMA: An harbe 'yan fashi da makami 32 tare da cafke 299 a jihar Legas

Tsoho yake cewa, hukumar ta bayar da kididdigar yadda za a kasafta kudin, inda wasu da suka gudanar da aikin hajjin su zasu samu nasu kason duba da rashin samun biyan bukata wanda nauyin hukumar ne sauke musu shi.

Ya kara da cewa, hukumar tana bukatar alhazan da su garzaya cibiyoyin da suka sayi kujerun su a kananan hukumomin su tare da fasfo domin karbar kudaden su.

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel