Kungiyar matan Sojojin Najeriya sun kai tallafin kayan jin kai gidan yara marasa galihu (Hotuna)

Kungiyar matan Sojojin Najeriya sun kai tallafin kayan jin kai gidan yara marasa galihu (Hotuna)

Kungiyar matan mayakan rundunar Sojojin kasa na Najeriya, NAOWA, ta kai tallafin kayan agaji gidan marayu da marasa galihu a shirye shiryenta na bikin tunawa da mazan jiya.

Legit.ng ta ruwaito baya da gidan marasa galihu, matan sun kai ziyara asibitin koyarwa na jami’ar Ibadan, inda suka kai tallafin kayan aiki, tare da tallafa ma marasa lafiya.

KU KARANTA: An sha ɗauki ba daɗi tsakanin wasu gungun yan fashi da jami’an Yansanda, guda 2 sun halaka

Kungiyar matan Sojojin Najeriya sun kai tallafin kayan jin kai gidan yara marasa galihu (Hotuna)

Ziyarar

Shugaban kungiyar, Umma-Kulsum Tukur Buratai ta ce babu yadda za’a yi kungiyar ta cimma muradunta ba tare da ta taimaka ma gajiyayyu dake cikin al’umma ba, sa’annan ta kara da cewa wannan tallafi sun yi shi ne don wayar da kan jama’a kan rayuwa cikin koshin lafiya ta hanyar tsare kai da kai.

Kungiyar matan Sojojin Najeriya sun kai tallafin kayan jin kai gidan yara marasa galihu (Hotuna)

Ziyarar

Shugaban Asibitin, Farfesa Temitope O Alonge, ya gode ma kungiyar, sa’annan ya bayyana tallafin ya zo a daidai lokacin da suke bukatarsa, shugaban wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Clement Abu ya jinjina ma rundunar Soji, saboda kokarin da take yi na zamar da Najeriya dunkulalliyar kasa.

Kungiyar matan Sojojin Najeriya sun kai tallafin kayan jin kai gidan yara marasa galihu (Hotuna)

Kayan

A can gidan marasa galihu, mai suna ‘Jesus Kids Autism Centre’, uwargidar Buratai ta yaba ma shugaban gidan marayun, da ilahirin ma’aikatan gidan, sakamakon namijin kokarin da suke yi wajen biyan bukatun yaran.

Kungiyar matan Sojojin Najeriya sun kai tallafin kayan jin kai gidan yara marasa galihu (Hotuna)

Ziyarar

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel