Nigerian news All categories All tags
Ku ajiye makaman ku, ku mika wuya - Sabon kwamandan Ofireshon Lafiya Dole ya shawarci mayakan kungiyar Boko Haram

Ku ajiye makaman ku, ku mika wuya - Sabon kwamandan Ofireshon Lafiya Dole ya shawarci mayakan kungiyar Boko Haram

- An canja kwamandan rundunar sojin Najeriya dake yaki da mayakan kungiyar Boko Haram a Maiduguri

- Sabon kwamandan ya shawarci mayakan kungiyar da su ajiye makaman su kuma su mika wuya

- Nicholas ya fara aiki ne ranar Litinin

Sabon kwamandan rundunar Ofireshon Lafiya Dole dake yaki da mayakan kungiyar Boko Haram a jihar Borno, Manjo Janar Rogers Nicholas, ya shawarci 'yan Boko Haram da su ajiye makaman su tare da mika wuya.

Ku ajiye makaman ku, ku mika wuya - Sabon kwamandan Ofireshon Lafiya Dole ya shawarci mayakan kungiyar Boko Haram

Sabon kwamandan Ofireshon Lafiya, Manjo Janar Rogers Nicholas.

Nicholas ya yi wannan kira ne a yau Laraba, yayin da yake rangadin gaisawa da jama'a a garin Maiduguri da kuma dakarun soji, bayan da ya karbi aiki daga hannun tsohon kwamandan rundunar, Manjo Janar Ibrahim Attahiru, ranar Litinin.

"Ina kira ga jama'a da su bawa sojojin Najeriya goyon baya. Muna bukatar hadin kan ku, musamman a bangaren samar da jami'an mu da sahihan bayanai". Inji Nicholas.

Sannan ya kara da cewa "hatta mayakan kungiyar Boko Haram ina basu shawarar su ajiye makaman su, kuma su mika wuya".

DUBA WANNAN: Gwamnatin APC ta saki jerin hanyoyi da gadoji da ta kammala cikin shekaru 2 kacal a mulki

Nicholas ya shaidawa jama'a cewar hukumar sojin Najeriya ta gama shirin kawo karshen aiyukan ta'addanci da sunan addini a yankin arewa maso gaba tare da tabbatar musu cewar nan bada dadewa ba dakarun soji zasu gama da mayakan kungiyar Boko Haram. Hakazalika Nicholas ya ce hukumar sojin za ta inganta walwalar sojojin dake aikin tabbatar da zaman lafiya a yankin arewa maso gabas.

A yayin rangadin da ya yi, Nicholas, ya ziyarci rundunar soji ta bakwai, cibiyar ajiye masu laifi ta hadin gwuiwar jami'an tsaro (JIDC), da asibitin sojoji.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel