Nigerian news All categories All tags
Kwararrun ma'aikata na musamman na Sufeto Janar sun cafke miyagu 5 a garin Aba

Kwararrun ma'aikata na musamman na Sufeto Janar sun cafke miyagu 5 a garin Aba

Ma'aikatan tsaro na musamman da Sufeto Janar na 'yan sanda Ibrahim Idris ya tanadar, sun cafke miyagu 5 masu garkuwa da mutane da suka addabi al'ummar garin Aba dake jihar Abia.

Legit.ng ta kawo muku sunayen wadannan 'yan ta'adda da biyar tare da inkiyar wasun su da sanadin jaridar Leadership kamar haka; Samuel James (Chiboy) mai shekaru 29, Justice Iriah (Mopol) mai shekaru 23 kuma dan asalin jihar Edo, Ikechukwu Igwebuike (Anambra) mai shekaru 22, Chikachi Ubani mai shekaru 30 da kuma Chineye Mark mai shekaru 45.

A rahoton kakakin rundunar 'yan sanda na jihar, Jimoh Moshood ya bayyana cewa, an cafke wadannan miyagu ne a ranar 11 ga watan Nuwamba na shekarar 2017, a sakamakon bin diddigin yadda suka yi garkuwa da wani dattijo, Cif Felix Ogbonna mai shekaru 80 da kuma neman kudin fansar sa.

Kwararrun ma'aikata na musamman na Sufeto Janar sun cafke miyagu 5 a garin Aba

Kwararrun ma'aikata na musamman na Sufeto Janar sun cafke miyagu 5 a garin Aba

Yake cewa, miyagun sun amsa laifin su a yayin da suka shiga hannu da cewar, sun fara wannan tabargazar ne a watan Nuwamba na shekarar 2017, kuma suke da alhakin garkuwa da mutane a lokuta uku daban-daban wadanda suka karbi fansar Naira 250, 000, naira Miliyan 1 da kuma naira miliyan 5.5.

KARANTA KUMA: Wani mahaifi ya dankarawa 'yar sa mai shekaru 10 ciki a jihar Legas

Kakakin 'yan sandan ya kara da cewa, wadannan 'yan ta'adda sun rarrabawa kawunan su ayyuka daban-daban domin samun nasarar aiwatar da ta'asar ta su cikin sauki. Ya kuma ce an karbo muggan makamai da dama tare da motoci biyu na gudanar da tabargazar su masu kirar Lexus Jeep da kuma Toyota Sienna.

LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel