Nigerian news All categories All tags
Wasu ma'aikatan hukumar lantarki sun sha cizo da duka a hannun wata mata

Wasu ma'aikatan hukumar lantarki sun sha cizo da duka a hannun wata mata

- Matar ta fada musu da duka ne bayan sun yanke wutar gidan ta da sukace bata biya ba tun Janairun wannan shekaran

- Bayan matar da fara dukan su, wasu maza guda biyu sun taya matar nakada musu dukan

- Matar dai ta musanta zargin da ake mata kuma alkali ya dage sauraron karar har zuwa Janairun shekara mai zuwa

An gurfanar da Kemi Shopade mai shekaru 28 gaban kotun majistare da ke zaune a Ikeja Legas a dalilin cizo da duka ta nakada ma ma'aikatan hukumar lantarki 2 da suka zo yanke mata wuta a gidan ta da ke Alaguntan, Iyana-Ipaja a Legas.

Wasu ma'aikatan hukumar lantarki sun sha cizo da duka a hannun wata mata

Wasu ma'aikatan hukumar lantarki sun sha cizo da duka a hannun wata mata

Mai shigar da karar, Sajent Godwin Awase yace matar tare da wasu mazu 2 wanda har yanzu ba'a gano inda suke ba sun doki mai'akatan hukumar lantarkin su biyu, Mista John Oluwole da kuma Mr Uwaoman Ibiam.

DUBA WANNAN: Hotuna: Masu zanga-zanga sun yi cincirindo a Majalisar Dokoki bisa kudirin kafa dokoki a kan kungiyoyi masu zaman kansu

Ya cigaba da cewa ma'aikatan dai sun je yanke wutar nata ne domin matar bata biya kudin lantarki ba tun daga watan Janairun wannan shekarar har izuwa yanzu. Bayan sun yanke wutar ne sai ta fada su da duka sannan sauran mazan 2 suka taya ta dukan nasu kuma daga bisani har ta cije su.

Matar ta musanta duka zargin da mai shigar da karar ya karanto kuma kotu ta bada belin ta a kan kudi N20,000 tare da mutane 2 da zasu tsaya mata a matsayin surety.

Alkalin kotun, Mr J.A Adigun ya dage sauraron karar har zuwa 5 ga watan Janairu na 2018.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel