Nigerian news All categories All tags
Yadda Gwamnoni su kayi kutun-kutun wajen karbe Jam’iyyar PDP

Yadda Gwamnoni su kayi kutun-kutun wajen karbe Jam’iyyar PDP

- Gwamnonin PDP sun yi kokarin karbe Jam’iyyar yayin da ake shiryawa 2019

- Nyesom Wike yayi kutun-kutun waje nada Uche Secondus a matsayin Shugaba

- Hakan zai ba Ahmad Makarfi damar samun tikitin Jam’iyyar a zabe mai zuwa

Yanzu haka mun samu cikakken labari cewa Gwamnonin Jam’iyyar PDP karkashin Gwamna Nyesom Wike sun yi kutun-kutun na karbar ragamar Jam’iyyar yayin da zaben 2019 ya karaso.

Yadda Gwamnoni su kayi kutun-kutun wajen karbe Jam’iyyar PDP

Gwamna Nyesom Wike ya daura Secondus

Jaridar Daily Trust ta bi diddikin yadda Gwama Wike su ka yi kokari wajen nada Prince Uche Secondus a matsayin Shugaban PDP. Ana zargin Wike da kashe makudan Biliyoyi domin ganin ‘Yan Jam’iyyar sun zabi Secondus da sauran mutanen sa a matsayin Shugabannin Jam’iyyar.

KU KARANTA: Yadda wani ya hango cewa Atiku zai koma PDP shekaru 2 da su ka wuce

Wike dai yana ganin cewa babu abin da Yarbawa za su iya tabukawa a Jam’iyyar PDP don haka ne ya goyi bayan Uche Secondus wanda ya fito daga Kudu-maso-kudancin Kasar. Akwai yiwuwar cewa nada Secondus zai ba tsohon Shugaban na rikon kwarya Makarfi samun tikiti a 2019.

Sai dai hakan zai kawowa tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar cikas wanda ya dawo Jam’iyyar PDP ana daf da zaben. Bisa dukkan alamu dai Atiku zai nemi takarar kujerar Shugaban Kasa a zaben 2019 inda zai nemi ya kara watakila da Shugaban Kasa Buhari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel